Manyan kamfanonin duniya na buƙatar finafinan Kannywood, inji shugaban MOPPAN mai murabus

DAGA MUHAMMADU MUJITTABA KANO   

“Daga cikin sauye-sauye da Kannywood ta samu a zamani shugabancina shine samun canje canje kasuwancin fina-finai wanda aka dai na cinikin ga wuri ga waina aka koma ta kamfanonin sadarwa na zamani irinsu YouTube, wanda yanzu akwai sama da 500 mai makon da ake saida a CD da makamantansu yanzu an wuce wannan an samu cigaba kuma yanzu akwai manyan kamfanonin duniya irinsu Amazon da suke bukatar finafinan Kannywood, wanda wannan abin farin ciki ne da nasarori da aka samu a zamani na,” cewar Dakta Ahmad M. Sarari, Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) mai barin gado na kasa.

Tsohon Shugaban MOPPAN, Dakta Ahmad Muhammad Sarari, ya bayyana haka ne a yayin tattaunawa da manema labarai na bankwana da matsayinsa na shugaban MOPPAN na kasa da ya ajiye shugabanci a qarshan wannan wata na farko a shekarar 2024.     

Haka kuma Dakta Sarari, da ya zayyano irin nasarorin da ya samu wanda ya yi alkawari tun kafin a zave shi a 2019, wadanda suka hada da dawo da darajar wannan kungiya musamam a idon gwamnati da hukumomi na kasa da dawo da rijistar MOPPAN ta hukumar kula da kamfanoni ta kasa, wato CAC, sai dawo da sunan qungiyar kan manhajar hukumar.

“Bugu da qari na samu nasarar gyara kundin tsarin mulkin kungiya, ba wa kungiyar kwararru taka rawa a zavan MOPPAN na qasa, farfaɗo da harkar kasuwancin fim a masana’antun Kannywood, horar da ‘yan quingiya wajen kara musu ilimi da dabarun yin fim, sanar da ‘yan masana’antu duk irin halin da kungiya ko masana’anta take ciki. 

Wani abin a gode wa ubangiji shi ne, samun cikakkiyar nasara akan ƙudirori na ɗaya harzuwa na biyar. An gudanar da kudirori na shida da na bakwai amma ba dari bisa dari xari ba,” inji shi.

Sai dai kuma Dakta Ahmad Sarari ya nuna damuwar sa kan yadda hukumomin gwamnatin jihohi da na Tarayyar Nijeriya suka yi shakulatun bangarorin da rashin kula da masana’antar finafinai, duk da kasancewar banda harkar noma babu wata masana’anta da take bada aikin yi ga matasa a Najeriya kamar harkar finafinai, domin suna bada kashi 1.25 na arzikin kasa da ake kira GDP da Turanci. 

“Wannan matsala ta watsi da harkar finafinai da rashin kulawa da gwamnati ta yi da harkar na daga cikin manyan kalubale da na fuskanta a matsayina na wanda ya rike kungiyar ta masu shirya finafinai ta Najeriya,” a cewar Sarari.

Shugaban Kungiyar MOPPAN, mai ritaya Dakta Ahmad Sarari, ya ce wani babban kalubale da ya fuskanta a lokacin shugabancin sa har sau biyu a wannan kungiya ta MOPPAN shi ne, rashin fahimta daga ‘yan kungiya na rashin sanin hakikanin meye hakjinsu a kungiya kuma meye hakin kungiya a kansu, wannan na daga cikin kalubale a wannan shugabanci na sa.

Tun daga farko shugaban MOPPAN mai barin gado sai da ya bayana cewa, “duk abinda yake da farko yana da karshe, Allah ne kadai ba shi da farko ba shi da karshe, kamar yau ne ‘yan wannan masana’anta suka nemi na fito takara zama shugaban kungiyar MOPPAN na qasa, na amsa kira aka yi zaven kuma na samu nasara sannan wa’adin farko ya kare a ka sake nemana a sake tsayawa duk da an san ba ni da ra’ayin hakan.”

Tsohon Shugaban MOPPAN ya ce, “shugabanci na kunshe da kalubale da kuma abin faranta rai abin da ya fi faranta muin rai a shuganci na shi ne, amincewa da amana da ‘yan kungiyar suka nuna mi ni domin ban yi takara da kowa ba, haka a hawa na biyu aka ce dole sai na yi karo na biyu da na nuna rashin yarda har sa baki manya suka yi ciki kuwa harda gwamna, wannan ba karamin amincewa aka yi min ba, kuma babban abin alfahari ne da farin cikin da bazan manta ba a matsayi na na shugaban kungiyar masu shirya finafinai ta Najeriya ba.

Ajiye shugabanci da na yi daidai ne duk da dai taron koli na wannan qungiya ta MOPPAN da aka yi a watan Yuni, na shekarar da ta gabata ya amince da karin shekara guda ga shugabanni na kasa da jihohi bisa tsari da ke cikin sabon kundin tsarin mulki na MOPPAN. Sauka ta daga mukami bai yi karo da taron koli ba hakan yana da alaqa ne da ra’ayi na, don haka sauran zababbu zasu ci gaba da shugabanci a karkashin jagorancin daya daga cikin mataimakana wanda yake kula da bangaren Arewa ta Tsakiya, wato Malam Habib Muhammad Barde, har zuwa shekarar 2025 in Allah ya kaimu.

Mun dauki alkawarin yin dukan wani aiki bisa kundin mulkin MOPPAN kuma mun yi alkawarin rike amanar wannan kungiya. Ina godiya ga Allah Madaukakin Sarki da dukanin shugabanin MOPPAN da suka gabata.” 

A karshe shugaban MOPPAN ya ce, “akwai cikakken bayanin ayyuka sama da dari da irin nasarori da kalubale da gazawa da aka samu a lokacin wannan shugabanci, kuma ni a matsayina na shugaban da ya gabata a shirye nake na bai wa sabon shugaba gudunmawa na ba su dukkan wani bayanai da suka bukata.

A karshe ina neman gafara ga duk wanda na batawa ko ina sane ko ba da sani na ba, ni ma na yafewa duk wanda ya batamun ko yana sane ko ba ya sane. Ina addu’a da fatan ubangiji ya taimaki Kannywood ya sada mu da dukanin alkairai da ke cikin wannan masana`anta, ya kuma kare mu da sharin da ke cikinta, ya kare jaharmu, ya kare kasarmu da ma duniya bakidaya. Allah ya bamu lafiya da zama lafiya.”