Hukuncin Kotun Ƙoli: Ban ƙulla wata yarjejeniya da Tinubu ba – Gwamna Abba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano a ranar Litinin ya karyata rade-radin dake yi na cewa ya kulla yarjejeniya da Fadar Shugaban Kasa gabanin hukuncin da Kotun Koli ta yanke ranar 12 ga watan Janairu wanda ya tabbatar da zabensa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktansa na yada labarai da bayanai, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a Kano a ranar Litinin.

Dawakin-Tofa ya bayyana wata takarda da tuni ta ke yawo tare da nuna wasu yarjejeniyoyi hudu tsakanin gwamna da fadar shugaban kasa a matsayin wata tatsuniyar da ba ta da tushe balle makama.

Ya bukaci jama’a da su yi watsi da rade-radin yarjejeniyar a matsayin karya da ke ikirarin gwamnan ya amince da tsallakawa jam’iyyar APC mai mulki da sauran sharuddan yarjejeniya.

“Gwanma Yusuf ya bayyana karara cewa kasancewar ya samu nasarar zabensa ta hanyar kuri’u na al’ummar Kano, da kuma tabbatar da hukuncin kotun koli, ba zai razana daga duk wani tuggun siyasa ba.

“Bari kuma in tunatar da wadanda suka maida siyasa sana’a da ke fakewa a karkashin sassaucin shugaban kasa cewa duk wata shawara ko alkiblar siyasa da za a bi a Kano za a tabbatar da shi ne a cikin tsarin doka da ikon zartarwa da ya rataya a wuyan gwamnan,” in ji Dawakin Tofa.