Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata kididdiga da Kungiyar Transparency International ta fitar kan rashawa ta nuna cewa an samu ci gaba wajen yaki da matsalar a Nijeriya inda a yanzu jasar ke mataki na 145 cikin kasa 180 da aka yi nazari a kai.
Kididdigar ta nuna cewa Nijeriya ta kara maki daya kan maki 24 da take da shi a baya inda a yanzu take da maki 25 cikin 100 baya ga matsawa daga matsayinta na 150.
Kididdigar na duba yadda yanayin matsalar rashawa take a gwamnatin kasashen da aka yi nazarinsu.
Tana bai wa kowace kasa maki daga 0 zuwa 100 – 0 na nufin matsalar rashawa ta yi katutu yayin da 100 ke nufin nasara a yaki da rashawa.
Cibiyar Rajin Kyautata Ayyukan Majalisun Dokoki da Yaqi da Rashawa a Nijeriya CISLAC wadda ta gabatar da jadawalin a Abuja, ta ce makin da Nijeriya ta samu kasa yake da maki 33 na kasashen da ke Kudu da hamadar sahara.
Jadawalin bai fito da bayanan rashawa ba a kasar amma ya bayyana yadda ake kallon cin hanci a Nijeriya.
CISLAC ta ce kididdigar ba wai tana nazarin ayyukan hukumomin yaki da rashawa ba ne da ta ce suna kokari wajen yakar cin hanci a Nijeriya.
