Gwamna Nasir ya amince da biyan Naira billiyan 27.5 ga ɗalibai ‘yan asalin Jihar Kebbi 

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi 

Gwamnan jihar Kebbi Dr. Nasir Idris, Kauran Gwandu ya amince da fitar da N27,500,000 domin  gaggauta biyan kudaden daliban da ke karatu a makarantar shari’a a Nijeriya tare da rijistar dukkan ‘yan asalin jihar Kebbi 38 dake wannan makarantar. 

Wannan yana qunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan shari’a na jihar Dr. Junaidu Bello Marshal wanda ya raba wa manema labarai a Birnin Kebbi a ranar Litinin din da ta gabata. 

A cewar kwamishinan, dalibai 28 Bar Part II za su karvi kudi Naira 750,000 (Naira Dubu Dari Bakwai da Hamsin Kadai) kowane, yayin da daliban kashi na daya za su samu Naira 650,000 kowane.

Amincewar Maigirma Gwamna ya zama dole a lokacin da mahukuntan makarantar Shari’a ta Nijeriya suka kara kudin zuwa N476,000 yayin da na Bar Part II da N353,000.

Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a, Dakta Junaidu Bello Marshall, ya gode wa Gwamna Nasir bisa ga wannan karimci da aka yi masa, ya kuma tabbatar wa gwamnati da aniyarsu ta zama jakadu nagari a jihar.

Sun bayyana wannan karimcin da gwamnan ya yi a matsayin daya daga cikin alkawarinsa na  samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa.

Za a iya tunawa a shekarar 2017 ne gwamnatin jihar Kebbi ta biya kudin makarantar koyon aikin lauya ta Nijeriya da kuma  rijistar ‘yan asalin jihar a shekarar 2017.