Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya da takwararta ta Ohanaeze Ndigbo mai kare muradun al’ummar Igbo da wasu kungiyoyin farar hula sun bayyana rashin jin dadinsu game da tafiya zuwa Paris da Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi daidai lokacin da kasar ke fama da karuwar matsalar tsaro.
A ranar Laraba 24 ga Janairu ne Shugaba Tinubu ya tafi zuwa Faransa domin wata ziyara ta kashin kai.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar gabanin tafiyar, ta ce Tinubu zai koma Nijeriya cikin makon farko na watan Fabarairu.
Sai dai kungiyoyin a hirarsu da jaridar Daily Trust sun koka cewa babu gaskiya cikin sanarwar tafiyar la’akari da yadda aka kira tafiyar ta “kashin kai”.
Matakin kungiyoyin na zuwa ne bayan da shi ma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya soki Tinubu inda ya bayyana shakku game da makasudin tafiyar tasa zuwa Faransa yayin da ake fuskantar karuwar matsalar ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro da ke ci gaba da ta’azzara.
Sai dai Fadar Shugaban Kasar ta ce duk da cewa Tinubu ba ya kasar, yana aiki tukuru domin kawo saukin matsalolin kuma yana bai wa hukumomin tsaro dukkanin goyon bayan da suke bukata domin samun nasara kan masu aikata miyagun laifuka da nufin fitar da Nijeriya daga halin rashin tsaron da take ciki.
Tinubu dai ya sa kafa ya fice daga kasar yayin da ake tsokaci game da jerin hare-haren da aka kai a Filato da sace-sacen jama’a a Abuja, babban birnin kasar da kuma hari na baya-bayan nan na sace dalibai da malaman makaranta a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Nijeriya.
Kungiyar Dattawan Arewacin Nijeriyar ta ce tafiyar ta Tinubu zuwa Faris a irin wannan yanayi da ake ciki a kasar manuniya ce cewa shugaban ya dukufa ne wajen cimma kudurorinsa na kashin kai a maimakon bai wa ‘yan Nijeriya kwarin gwiwa a lokacin da suke bukatar hakan.
Daraktan yada labarai na kungiyar, Abdulazeez Sulaiman ya ce kungiyar tana ganin matakin na shugaban kasar na tabbatar da damuwar da ake nunawa cewa Nijeriya ta fada cikin matsalar rashin shugabanci nagari da rashin nuna damuwa da tausayi.
A nata bangaren, kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yi allah-wadai da tafiyar ta Shugaba Tinubu zuwa Faris a halin tabarbarewar tsaro da sauran kalubale da ake ciki.
Babban sakataren kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro ya ce bulaguron da Tinubu ya yi na zuwa ne a lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen tattalin arziki.
Isiguzoro ya yi kira ga Tinubu da ya yi wa yan Nijeriya bayani dalilin yin irin wadannan tafiye-tafiye.
Shi ma shugaban kungiyar tabbatar da jagoranci nagari, GGT, Mista Tunde Salman ya ce da alama Shugaba Tinubu ya bai wa wasu manyan jami’ai har da mataimakin shugaban kasa damar tafiyar da al’amuran.
Ya ba da misali da wani kwarya-kwaryan taro da aka shirya kan tsaro game da karuwar matsalar a Arewacin Nijeriya, inda mataimakin shugaban kasa da ministocin tsaro suka zama masu taka rawa sosai a taron.
