Babaji

4771 Posts

Mafi ƙarancin albashi: Yayin da ake ƙarƙare batun a ranar Litinin, gwamnati ta gabatar da naira 62,000 ga NLC da masu ruwa da tsaki

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A yau Litinin ne ake sa ran kammala batun ƙayyade mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata a Najeriya, yayin da ƙungiyoyin ƙwado ke sauraron amsar tayin naira 250,000 daga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta yi. Shuwagabannin ƙungiyoyin ƙwado na ƙasa sun bada wa'adin 10 ga watan yuni a matsayin ranar ƙarshe da zasu saurari amsar gwamnatin tarayya game da batun. A ranar Jumma'ar da ta gabata ne kwamitin ƙayyade ƙarancin albashi ta ƙasa ta gudanar da wani zama, inda aka cimma yarjejeniyar naira dubu 62 tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da kuma na haɗaɗɗiyar kungiyar ma'aikatu masu…
Read More