Babaji

4771 Posts

Johnathan ya jinjina wa gwamnan Edo kan 70,000 mafi ƙarancin albashi a Jiharsa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yaba ma gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki kan amincewa da biyan naira dubu saba'in a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan Jiharsa. Ya faɗi haka ne a ranar Laraba yayin hira da manema labarai a lokacin ƙaddamar da buɗe sabon sakatariyar ma'aikata a Benin, babban birnin Jihar. Johnathan ya ce, wannan wani mataki ne da zai inganta walwala da jin daɗin al'ummar Jihar da kuma gwamnatinsa. Goodluck ya ƙara da cewa kasancewarsa jajirce kuma mai hangen nesa ne suka sa ya yi wannan babban abun a yaba duk…
Read More

Shugaba Tinubu Mutum ne kamar kowa: Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai na musamman, Bayo Onanuga ya kare shugaba Tinubu biyo bayan tuntuɓe da ya yi a filin taron 'Eagle Square' dake Abuja a ranar Laraba. A yau ne demokradiyyar Najeriya ke cika shekaru 25 inda shugaba Tinubu ya haɗu da jarabawar faɗuwa gabannin fara jawabinsa a filin taron Bayo, ya ce faruwar hakan kan auku da kowa kuma a kowane lokaci inda ya bada misali da Biden da Obama na Amurka waɗanda irin haka ya sha faruwa da su, dan haka lamarin bai da tasiri wajen gudanar da ayyukan…
Read More

Shugaba Tinubu yayi tuntuɓe a ‘Eagle Square’

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da ake bikin cikar demokradiyya shekaru 25 a Najeriya, shugaba Bola Ahmed Tinubu yayi faɗuwar ba zata a lokacin da yake ƙoƙarin hawa matakalar motar zagaye a filin taro na 'Eagle Square' dake Abuja. Rahotanni sun bayyana cewa, babu wani rauni ko ɗimuwa da Tinubu ya samu a lokacin aukuwar lamarin inda nan-da-nan aka ga ya cigaba da jawabi kan al'amurran da suka shafi taron da sauran abubuwa. A wani rubutu da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai a kafafan sada zumunta, Dada Olusegun yayi, an samu ƙarin haske kan batun inda ya ce…
Read More

Ado Bayero ya gayyaci Hakimai bikin durbar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero wanda gwamnatin Jihar ta sauke daga karagar mulki, ya gayyaci tawagar hakiman Jihar zuwa bikin wasan doki na durbar da ake gabatarwa a lokutan Sallah da ma wasu bukukuwan. Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi ya fitar da sanarwar a wata takarda dake ɗauke da sa hannunsa a ranar Talata inda take umurtan dukkan masarautun Jihar da su halarci taron da Hakimai da masukunta da kuma mawakansu a lokacin bikin sallah babba. Bayanin takardar, ya ƙara da cewa tana kira ga dukkan Hakiman masarautu da su hallara a fadar Aminu…
Read More

DSS ta gargaɗi masu zanga-zangar ‘June 12’

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI An gargaɗi mutane da su ƙauracewa dukkan nau'o'in zanga-zanga da ka iya haifar da tashin-tashina a tsakanin al'umma yayin gudanar da shagulan bikin murnar ranar demokradiyya wanda ake yi a ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara. Sanarwar ta fito daga bakin mai magana da yawun hukumar 'ƴan sandan farin kaya ta DSS, Dakta Peter Afunanya inda ya ce hukumar ba zata amince da dukkan nau'in tada-zaune-tsaye gami da karya doka da odar ƙasa ba. Peter ya ce, sun samu rahotanni dake batun cewa akwai mutane daban-daban da suka shirya gudanar da zanga-zanga a wurare da…
Read More

Hukumomin ƴan sanda da na soji na kawo cikas ga ƙoƙarina wajen magance matsalar tsaro: Gwamnan Zamfara

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan Jihar Zamfara dake Arewa-maso-Yammacin ƙasarnan, Dauda Lawal ya koka kan yadda jami'an ƴan sanda da na soji ke haifar da koma baya wajen ganin an daƙile ayyukan ƴan ta'adda da ke addabar Jihar tsawon lokaci. Dauda ya ce rashin bin umurnin gwamnatin tarayya ga hukumomin kan matsalar ke da alhakin gefa Jihar cikin mawuyacin halin da take ciki a yau ganin yadda al'umma suka gagara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tsawon shekaru. A cikin wata hira da gidan talabijin na 'channels' a ranar Talata, ya ce kasancewar bashi da iko kan dukkan ɓangarorin jami'an…
Read More

Kwalara ta yi sanadiyar mutuwar mutane biyar a Legas

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rahotanni daga Jihar Legas na cewa a ƙalla kimanin mutane biyar ne suka mutu yayin da aka garzaya da mutum sittin asibiti sakamakon ɓullar cutar kwalara a yankunan Eti Osa, Lagos Island, Ikorodu da kuma Kosofe. Kwamishinan ma'aikatar lafiya na Jihar, Farfesa Akin Abayomi ya fadi a lokacin fitar da wani rahoto na musamman kan aukuwar lamarin inda ya ce gwamnatin jihar ta samar da hanyoyin hana cigaba da yaɗuwar cutar. Akin ya kuma bayyana cikin alhini cewa wadanda suka mutu an same su ne cikin mutanen da aka kai su asibiti a ƙurarren lokaci. Bugu-da-ƙari,…
Read More

Atiku yayi Alla-wadai da kashe mutane 50 a Katsina

Daga Umar Garba Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen shekarar 2023, Atiku Abubakar ya yi Alla-Wadai da harin da ƴan bindiga suka kai a ƙauyen ƴar Goje dake Ƙaramar hukumar Ƙanƙara a Jihar Katsina wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama. "Ina mai cike da baƙin ciki game da samun labarin harin da aka kai ƙauyen Ƴar Goje dake ƙaramar hukumar Ƙanƙara a Jihar Katsina, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama, tare da yin garkuwa da mata da ƙananan yara." Inji shi. Da yake nuna alhininsa game da…
Read More

Shugaba Tinubu ya naɗa Argungu a matsayin shugaban hukumar PSC

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa tsohon mataimakin sufetan ƴan sanda na ƙasa, Hashimu Argungu a matsayin sabon shugaban hukumar kula da harkokin ƴan sanda ta PSC. Argungu ya maye gurbin Solomon Arase ne da shugaba Tinubu ya tsige, wanda ke shugabantar hukumar tun watan Janairun 2023, a lokacin gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari. Sanarwar ta fito ne daga ofishin mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale a ranar Litinin. Haka nan, sanarwar ta ce Tinubu ya naɗa Chief Onyemuche Nnamani a matsayin sakataren hukumar da kuma Taiwo Lakanu mai ritaya a…
Read More

Yadda kotu ta dakatar da EFCC daga kama Kwankwaso

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata babbar kotu a Jihar Kano ta fitar da takardar hana kama ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar NNPP a babban zaɓen shekarar 2023, Rabi'u Musa Kwankwaso da wasu mutane bakwai, wacce ke ƙunshe da hana kamawa ko cin mutunci ko kuma tsare su. Mutanen sun haɗa da Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Clement Anele, Folshade Aliu, Buba Galadima da kuma Rabiu Musa Kwankwaso. Mai Shari'a Yusuf Ubale Muhammad ya fitar da takardar dake ɗauke da bayanin wanda ya fara aiki daga ranar 5 ga watan yunin shekararnan. Kotun ta ce ta ɗage sauraron ƙarar…
Read More