Atiku yayi Alla-wadai da kashe mutane 50 a Katsina

Spread the love

Daga Umar Garba

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2023, Atiku Abubakar ya yi Alla-Wadai da harin da ƴan bindiga suka kai a ƙauyen ƴar Goje dake Ƙaramar hukumar Ƙanƙara a Jihar Katsina wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama.

“Ina mai cike da baƙin ciki game da samun labarin harin da aka kai ƙauyen Ƴar Goje dake ƙaramar hukumar Ƙanƙara a Jihar Katsina, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama, tare da yin garkuwa da mata da ƙananan yara.” Inji shi.

Da yake nuna alhininsa game da faruwar lamarin, Atiku yayi ƙarin haske kan harin kwantan-ɓauna da maharan suka yi wa jami’an tsaron dake kai ɗaukin gaggawa a ƙauyukan Gidan Tofa da Ɗan Nakwabo wanda yayi sanadin mutuwar jami’an ƴan sanda huɗu da wasu jami’an tsaron al’ummar Jihar Katsina guda biyu.

“Abin da ya fi damuna shi ne, waɗannan ayyukan ƴan fashi da ta’addanci sun zama na yau-da-kullum, inda ga alama gwamnati bata da wani taimako da zata iya yi, duba da halin ko-in-kula da ta nuna a kai, duk kuwa da ɗimbin kasafin kuɗin tsaro na shekara-shekara da ake warewa.” Inji Atiku.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar yayi kira ga gwamnati da ta ƙara ɗaukar nauyinta na kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa da muhimmanci.

Ya kuma buƙaci da a ɗauki ƙwararan matakai na yaƙi da matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankin.Sannan, ya kuma bayyana alhininsa ga iyalan waɗanda abin ya shafa, inda ya buƙace su da su ƙara ƙaimi a wannan mawuyacin lokaci.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, rahotanni suka bayyana cewa ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun afka wa ƙauyen da dare inda suka hallaka kimanin mutum 50 gami da sace wasu wadanda kawo yanzu ba a san adadinsu ba.

By Babaji