Shugaban ƙasar Malawi Lazarus Chakwera ya faɗa ranar Talata cewa ba a samu wanda ya rayu ba a cikin jirgin da ke ɗauke da mataimakinsa Saulos Chilima da kuma wasu mutum tara lokacin da jirgin su ya faɗi a wani daji.
Masu neman jirgin sun sami nasarar gano ɓarguzan jirgin lokacin da a ka nemi jirgin ba a gani ba.
Jirgin an neme shi ba a ganshi ba jiya Litinin lokaci da yakamata ya sauka a wani gari Mzuzu da ke arewacin ƙasar amma ya gaza hakan sabida yanayi marar kyau.
Wasu hotuna da gidan Jarida na AfP ya fitar sun nuna wasu sojoji na tsaye kusa da ɓaraguzan jirgin sojan mai lamba Dornier 228-202k
