Wasu Mahara da ake zargin yan boko haram ne sun yi garkuwa da fasinjoji da dama a kan hanyar Maiduguri zuwa kano. Maharan sun kai hari ne tsakanin garin Kuturu da ƙauyen Mannanari wanda ke kusa da ƙauyen Auno. Sun kai harin ne da yammacin litinin wajen karfe 5:50pm.
Al’amarin ya tsayar da zirga zirga kan titin na tsawon lokaci wanda ya tursasa wasu komawa garin Banisheik da Auno.
Wasu Mazauna Ƙauyukan sun bada labarin yadda masu motocin haya suka fake a garuruwansu domin jiran lokacin da sojoji zasu buɗe hanyar.
