Mafi ƙarancin albashi: Dalilan da ya sa ba za mu koma yajin aiki ba- Ƙungiyar Ƙwadago

Spread the love

Ƙungiyar Ƙwadago tace ba za ta koma yajin aiki ba a ranar 11 ga watan Yuni kan tattaunawar ta da gwamnatin tarayya a kan mafi ƙarancin albashi.

Shugaban ƙungiyar Ƙwadagon, Joe Ajaero ne ya sanar da haka a wani taron ƙasa da ƙasa a birnin Geneva, Switzerland.

Ajaero ya jaddada cewa, alƙaluman suna gaban shugaban ƙasa, don haka ba za su iya tafiya yajin aiki yanzu ba. “Muna jiran mu ji me shugaban ƙasa zai ce sannan mu zauna taron masu ruwa da tsaki a ƙungiyar Ƙwadagon don sanin menene kuma zamuyi a gaba.”

Sannan Ajaero ya soki wasu gwamnoni da suke faɗin ba za su iya biyan sabon mafi ƙarancin albashin ba. Yana mai tuhumar su da cewa su tayaya suke biyan kansu?

” A ina gwamnan Edo Godwin Obaseki ya ke samun 70,000 na biyan mafi karancin albashi? Irin waɗannan gwamnoni sune abun koyi ba marasa jajircewa ba.”

By ukarofi