Babaji

4774 Posts

Kwamishinan ‘Yan sandan Kano ya musanta zargin su na ƙin biyayya ga gwamnatin Jihar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kwamishinan 'Yan sandan Jihar Kano, Ussaini Gumel ya ce bai taɓa ƙin girmama gwamnatin Jihar ba, biyo bayan kalaman Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari'ar Jihar, Haruna Dederi a kansu na cewa suna ƙoƙarin yin tawaye gami da bijirewa shugabancin gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf. A ranar Asabar da ta gabata ne, Dederi ya yi magana a kan hukumar inda ya bada misali da sanar da dakatar da bukukuwan sallah da ta yi ba tare da umurni ko sanar da gwamnatin Jihar ba wanda hakan ya sa suka nuna rashin jin daɗinsu ga hukuncin. Kwamishinan, ya musanta…
Read More

‘Yan bindiga sun kashe mutum 10 a Sakkwato ranar sallah

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI An samu rahoto daga Jihar Sakkwato dake cewa ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Dudun Doki a ƙaramar hukumar Gwadabawa da asuban ranar Lahadi. Yayin da al'ummar musulmi ke bikin sallah, mutanen ƙauyen sun kasance cikin jimami da alhini ganin cewa ƴan bindiga suka kashe kimanin mutane goma tare da yin garkuwa da wasu da dama waɗanda kawo yanzu ba'a san adadinsu ba. Jaridar Alfijir ta ruwaito cewa, ƴan bindigan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare.
Read More

‘Yan Sandan Kano na karɓar umurni daga wasu ɓoyayyun mutane – Gwamnatin Jihar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Jihar Kano ta nuna damuwa kan yadda jami'an 'Yan Sanda ke bijire wa karɓar umurni ta hanyar da doka ta tsara inda take zargin wasu mutane da ba huruminsu bane ke juya hukumar. Kwamishinan Shari'a kuma Antoni Janar na Jihar, Haruna Isa Dederi ya faɗi hakan a wani taron manema labarai inda ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf shi ne shugaban harkar tsaron Jihar kuma ke da ikon umurtar dukkan hukumomin tsaron Jihar. Dederi ya ce, wasu mutane da ba a san ko suwaye ba suna bada umurni ga hukumar 'Yan Sanda inda ya bada…
Read More

Rikicin Masarautar Kano – Kotu za ta yi hukunci kan ƙarar soke dokar tsarin Masarautun Jihar na 2024

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata babbar kotu a Jihar Kano ta ayyana ranar Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2024 a matsayin lokacin da za ta yanke hukunci kan sabuwar dokar Masarautu da gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf ya ƙirƙira. Mai Shari'a Abdullahi Muhammad Liman ya bada sanarwa kan ƙarar wanda Sarkin Dawakin Masarautar, Aminu Baba Ɗan Agundi ya shigar kan sauya dokar zuwa yadda tsohuwar gwamnatin Jihar ta tsara. Hakan na zuwa ne biyo bayan da Sarkin Dawakin ya ce Gwamnatin Jihar ta ki girma 'yancinsa na ɗan ƙasa inda yake neman kotun da ta tabbatar da adalci kan rikicin…
Read More

Zamfara ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatanta

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da ake cigaba da shirye-shiryen bikin babbar sallah, gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya ƙaddamar da fara biyan naira dubu 30 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata a Jihar. Jawabin ya fito ne daga bakin mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a inda ya ce sun yi haka ne sakamakon cika alƙawarin da suka yi tsakaninsu da wakilan ƙungiyar ƙwadago na Jihar a watan da ya gabata. Sanarwar ta ce, tuni dai ma'aikata suka fara karɓar albashi kan sabon tsarin daga ranar 12…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun hutun sallah

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ware ranakun Litinin da Talata a matsayin lokacin hutun bikin Babbar-sallah a faɗin ƙasar. Babbar sakatariyar ma'aikatar harkokin cikin gida, Dakta Aishetu Gogo Ndayako ta faɗi hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar juma'a. Dakta Aishetu ta ce, ministan ma'aikatar, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya inda ya ce yana mai taya al'ummar musulmi murnar zagayowar wannan lokaci mai albarka. Ya kuma yi kira ga al'ummar musulmi da su cigaba da kasancewa masu son zaman lafiya, da kyautatawa juna, da sadaukarwa tare da yin addu'o'in samun zaman…
Read More

Sufeta Janar ya dakatar da ƙarin girma na musamman a hukumar ‘Yan Sanda

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sufeta Janar na hukumar 'Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya sanar da dakatar da tsarin ƙarin girma na musamman da ake yi wa jami'ansu inda ya ce hakan na haifar da rauni da kawo cikas ga ƙoƙarinsu wajen gudanar da ayyukansu. Kayode ya bayyana hakan ne a yayin bikin girmama manyan jami'ai 15 da hukumar ta ƙara wa girma a Abuja. Kayode, ya bayyana alhininsa kan yadda wasu ma'aikatan ke kamun ƙafa wajen neman waɗannan muƙaman, dan haka ya ce duk wanda aka kama da yunkurin haka, to za'a hukunta shi. Ya kuma ƙara da cewa,…
Read More

Rikicin masarauta: Lauyoyin Gwamnatin Kano sun fice daga kotu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Bayanan da ke fitowa daga cikin Babbar Kotun Tarayya a Kano da ke sauraron ƙarar da ake yi kan rikicin Masarautar Kano sun nuna cewa, lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar Dokokin Jihar sun fice daga zauren kotun. Blueprint Manhaja ta gano cewa, wannan ya biyo bayan gabatar da takardar ɗaukaka ƙara da suka gabatar wa alƙalin kotun, Liman Muhammad ne kan hukuncin da ya yanke a jiya Alhamis, inda ya ƙi amincewa. Lauyoyin sun ɗaukaka ƙara ne bisa hukuncin da kotun ta yanke na huruminta kan sauraron ƙarar. To amma, Alƙali Liman ya ƙi yarda…
Read More

Ba mu amince da wasan kwaikwayon Gwamnatin Zamfara ba – Wasu ‘yan kishin Jihar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wasu masu fafutukar zaman lafiya da cigaban al'umma a Zamfara sun yi kira ga gwamnan Jihar, Dauda Lawal da ya daina siyasantar da mulkin 'yan Jihar tare da mayar da hankali wajen ayyukan da ya alƙawuranta wa mutane. Jaridar 'Daily Post' ta ruwaito cewa, ƙungiyar ta buƙaci gwamnan da ya bayyana wa al'ummar Jihar jadawalin nasarorinsa cikin shekara guda da yake kan karagar mulki. A cikin satinnan ne shuwagabanni a matakai daban-daban kama daga kan shugaban ƙasa zuwa gwamnoni suka bayyana ire-iren nasarorin da suka samu a yayin da suke bikin cikar shekara ɗaya a kan…
Read More

Har yanzu Aminu Ado Bayero na da ikon faɗa-a-ji – Kotu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata babbar kotu a Jihar Kano, ta ce har yanzu sarki Aminu Ado Bayero na riƙe da kambun sarautar dake nuna cewa yana da ikon faɗa-a-ji duk da cewa gwamnatin Jihar ta fitar da sanarwar rusa tsarin masarautun da tsohuwar gwamnati ta yi a baya. Mai Shari'a Liman Mohammed ya bayyana haka jim-kaɗan bayan wata sanarwa da ta fito daga wata kotun Jiha sakamakon ƙarar da gwamnatin Jihar take kai tana mai cewa Sarki Ado da wasu sarakuna huɗu basu da hurumin amsa sunayen sarakuna tunda gwamnatin Jihar ta soke tsarin masarautunsu da aka yi a…
Read More