Rikicin Masarautar Kano – Kotu za ta yi hukunci kan ƙarar soke dokar tsarin Masarautun Jihar na 2024

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wata babbar kotu a Jihar Kano ta ayyana ranar Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2024 a matsayin lokacin da za ta yanke hukunci kan sabuwar dokar Masarautu da gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf ya ƙirƙira.

Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya bada sanarwa kan ƙarar wanda Sarkin Dawakin Masarautar, Aminu Baba Ɗan Agundi ya shigar kan sauya dokar zuwa yadda tsohuwar gwamnatin Jihar ta tsara.

Hakan na zuwa ne biyo bayan da Sarkin Dawakin ya ce Gwamnatin Jihar ta ki girma ‘yancinsa na ɗan ƙasa inda yake neman kotun da ta tabbatar da adalci kan rikicin Masarautar.

Waɗanda ƙarar ta shafa sun haɗa da gwamnatin Jihar, da majalisar dokokin Jihar, da antoni Janar ɗin Jihar, da kwamishinan ‘Yan Sanda, da Sufeta Janar na ƙasa da kuma hukumomin jami’an ‘Civil Defence’ da na ‘DSS’.

By Babaji