Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar ƙorafe-ƙorafen Jama’a da Yaƙi da Cin Hanci ta ƙasa da Rashawa reshen Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu tare da gayyatar wasu sakatarorin dindindin guda uku domin amsa tambayoyi kan badaƙalar sayar da fom ɗin aiki a Ofishin Shugaban Ma’aikata.
Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa a Kano ranar Laraba cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike don gano tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a badaƙalar. Ya ce, tuni dubban masu neman aiki damfarar ta shafa.“Bincike na farko ya gano ayyukan damfara a ofishin shugaban ma’aikata, hukumar ma’aikata, hukumar kula da makarantun sakandire ta jihar Kano, da hukumar kula da harkokin kiwon lafiya.
“Mutane biyun da ake zargin da ake tsare da su suna bayar da hadin kai ga binciken, wanda ya kai ga rufe shafin ɗaukar aikin na bogi.“Hukumar tana ƙoƙarin kawar da cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da an yi adalci a badaƙalar neman aikin yi da ta damfari dubban masu neman aiki,” inji Rimin Gado.
