Shugaba Tinubu yayi kira da a samu alaƙa mai karfi tsakanin hukumomin yaƙi da ta’addanci na Najeriya da kuma hukumar leƙen asiri da ke ƙasar Amurka.
Shugaban yayi wannan kira ne a yayin ganawarsa da daraktan hukumar leƙen asirin Chritopher Asher a fadar shugan ƙasan da ke Abuja.
Manyan jami’an tsaro da suka halarci taron sun haɗa da, Malam Nuhu Ribado, Babban sufeton yan sanda, Kayode Efbetekun, shugaban hukumar yan sanda farin kaya, Yusuf Bichi, shugaban hukumar da ke yaƙi da fatucin miyagun ƙwayoyi, Birgediya Janar Buba Marwa, da sauransu.
Shugaban yayi murna ƙwarai dagaske da ziyarar. Wanda yace hakan yana nuni da irin alaƙa mai karfi dake tsakanin Najeriya da ƙasar Amurka wajen yaƙi da ta’addanci da sauran laifuka.
