
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Yayin da ake cigaba da shirye-shiryen bikin babbar sallah, gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya ƙaddamar da fara biyan naira dubu 30 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata a Jihar.
Jawabin ya fito ne daga bakin mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a inda ya ce sun yi haka ne sakamakon cika alƙawarin da suka yi tsakaninsu da wakilan ƙungiyar ƙwadago na Jihar a watan da ya gabata.
Sanarwar ta ce, tuni dai ma’aikata suka fara karɓar albashi kan sabon tsarin daga ranar 12 ga watan Yuni la’akari da bikin babbar sallah dake tafe.
Kafun wannan lokaci, ma’aikatan Jihar na karɓar naira dubu 7 ne a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Sanarwar ta ƙara da cewa, gwamnatin Jihar ta yi aiki tuƙuru wajen ganin ta biya albashin watanni uku da aka riƙe da ƙuɗaden hutun aiki da giratuti gami da kiyaye biyan ma’aikatan a kan lokaci.
Daga ƙarshe, ya ce gwamnatin za ta cigaba da ƙoƙarin tabbatar da samun walwala da jin daɗin ma’aikatanta ta hanyoyin da suka dace.
