Rikicin masarauta: Lauyoyin Gwamnatin Kano sun fice daga kotu

Spread the love


Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Bayanan da ke fitowa daga cikin Babbar Kotun Tarayya a Kano da ke sauraron ƙarar da ake yi kan rikicin Masarautar Kano sun nuna cewa, lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar Dokokin Jihar sun fice daga zauren kotun.

Blueprint Manhaja ta gano cewa, wannan ya biyo bayan gabatar da takardar ɗaukaka ƙara da suka gabatar wa alƙalin kotun, Liman Muhammad ne kan hukuncin da ya yanke a jiya Alhamis, inda ya ƙi amincewa.

Lauyoyin sun ɗaukaka ƙara ne bisa hukuncin da kotun ta yanke na huruminta kan sauraron ƙarar.

To amma, Alƙali Liman ya ƙi yarda da shaidar ɗaukaka ƙarar da suka gabatar masa a zaman kotun na yau Juma’a.

Hakan ya fusata lauyoyin, waɗanda suka fice daga kotun a fusace.

A cewarsu, tunda suka ɗaukaka ƙara, alƙalin ba shi da ikon cigaba da sauraron shari’ar har sai an ga abinda ya wakana a Kotun Ɗakaka Ƙara.

Tuni dai Liman ya cigaba da sauraron shari’ar a bayan idon masu ɗaukaka ƙarar.

By Babaji