A yau ne babbar Kotun Ƙasa da ke jihar Kano ta ci tarar gwamnatin Kano Naira Miliyan 10 sabida take haƙƙin dan adam da tayi wa sarkin da aka tuɓe Aminu Ado Bayero
Wannan na zuwa ne bayan da Alƙalin kotun Mai Shari’a Muhammad Liman ya bayyana cewa kotun na da hurumin sauraron ƙarar Aminu Ado ɗin.
Yayin da mai Sharia Simon Amobeda yake karanto hukunci a yau, Ya ƙara da cewa Aminu Ado na da yancin yin yawo cikin garin kano a ko da yaushe.
Sai dai kotun ba ta bada umarnin fitar da Sarki Sanusi daga gidan rumfa ba.
Sai dai mai wakiltar gwamnatin Kano yace wannan ma nasara ce saboda kotun bata soke dokar da ta kawo sarki Sanusi ba. Sannan yace zasuyi shawara domin ganin shin zasu ɗaukaka ƙara a kan tarar Miliyan 10 ko ba za suyi ba.
