Kotu ta sallami manyan masu ruwa da tsaki na Binance

Spread the love

Daga Karofi Usman

Babban kotun Ƙasa da ke zamanta a Abuja ta sallami Tigran Gambaryan, dan shekara 39 ɗan asalin ƙasar Amurka da kuma Nadeem Anjarwalla waɗanda ake zargi da rashin biyan haraji.

Dukkansu masu ruwa da tsaki a kafar da ake hada hadar kirifto wato Binance wanda gwamnatin Najeriya ke ƙara ta hannun hukumar FIRS a kan rashin biyan haraji.

Duk da cewa Binance ba tada wakili na doka a Najeriya, bai hana an karanta tuhume tuhemen ga Gambaryan ba.
Mai wakiltar shi yace wanda yake wakilata ba a bashi tuhumar ba hannu da hannu, don haka bai kamata a cigaba da shari’a ba alhalin wanda yake wakilta bai fahimci me ake tuhumar sa dashi ba.

By ukarofi