Babaji

4775 Posts

Trump ya yi alƙawarin katin ɗan ƙasa ga ƴan ƙasar waje da suka yi difuloma a Amurka

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ɗan takarar jam'iyyar 'Republican' kuma tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya yi alƙawarin mallaka wa dukkan ƴan ƙasar waje katin zama ɗan ƙasa matukar mutum ya yi karatun matakin difuloma a ƙasar. Trump, ya faɗi hakan ne a wata hira da ƴan jaridu, jim kaɗan bayan babban abokin hamayyarsa kuma shugaban ƙasar na yanzu, Joe Biden ya shelanta cewa za'a ƙwace matsayin ƴancin zama ɗan ƙasa ga duk waɗanda suka auri ƴan Amurka da ba ƴan ƙasa ba a ƙoƙarinsa na kawo ƙarshen magance matsalar zama ɗan ƙasa ba bisa ƙa'ida ba da wasu da…
Read More

Za a kammala aikin filin jirgin saman Gusau cikin wata uku-Gwamnan Zamfara

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ce za a kammala aikin filin jirgin saman Gusau cikin nan da wata uku. Gwamnan ya faɗi hakan ne a yayin taron buɗe aikin filin jirgin wanda Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya yi a Gusau, babban birnin Jihar a ranar Alhamis da ta gabata. A wani jawabi daga mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Sulaiman Idris, an ƙaddamar da aikin filin jirgin ne domin yin sufuri a cikin gida Najeriya da kuma ƙasashen waje. Ya ƙara da cewa, aikin zai ci tsawon kilomita 3 zuwa 4…
Read More

Aikin tashar ‘gas’ na AKK zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙin Arewacin Najeriya – Ministan Labarai

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ministan yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Mohammed Idris ya ce aikin tashar iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano, zai taimaka wajen inganta tattalin arziƙin Arewacin Najeriya. Ministan ya faɗi haka ne ta ofishin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Rabiu Ibrahim a yayin wani ziyaran gani da ido da ya kai wajen aikin a Jihar Kaduna tare da Ministocin kuɗi da tattali, Wale Edun da ƙaramin ministan albarkatun iskar gas, Ekperikpe Ekpo da kuma shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari. Ya kuma ce, aikin zai sa a samu yawaitar amfani da iskar gas a gidaje da wajen…
Read More

Gwamnatin Tinubu za ta sayo wa Fadar Shugaban Ƙasa sabon jirgi bayan gwanjon tsofaffin jirage uku

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar sayar da tsofaffin jiragen sama na ofishin shugaban ƙasa domin sayo sabo wa ofishin. Hakan ya faru ne bayan da kwamitin majalisar wakilai kan tsaron ƙasa da basira ya bada shawarar cewa akwai buƙatar a sayo jirage guda biyu domin amfanin shugaban ƙasa da na mataimakinsa. Shugaban kwamitin na ɓangaren majalisar dattijai, Shehu Buba Umar ya bada goyon bayansa kan shawarar majalisar wakilan. Rahoton ya ƙara da cewa, sayar da jiragen zai taimaka wajen samun daidaito kan adadin da ake buƙata a ofishin, domin yanzu haka akwai jirage gama gari guda…
Read More

An yi garkuwa da mai naƙuda akan hanyarta ta zuwa asibiti

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wata mata mai juna biyu dake gaf da haihuwa a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun. Lamarin ya faru ne da matar mai suna Ogunbunmi, a unguwar Oke Lantoro akan hanyarta ta zuwa asibiti a ranar Alhamis. Mijinta mai suna Mista Lateef Ogunbunmi ya ce ya ga saƙo ta 'wattsapp' cewa an yi garkuwa da matarsa daga waɗanda suka yi garkuwar da ita. Kakakin Rundunar Ƴan sandan yankin, Omolola Odutola ya tabbatar da labarin a lokacin da mijin matar ya shigar da ƙara a babban ofishinsu dake yankin Kemya inda…
Read More

Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta gargaɗi mutane kan ƙauracewa tashin-tashina – Rikicin Masarauta

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da babbar kotun tarayya da ke Kano ke yin hukunci kan wasu al'amura da suka shafi Masarautar Jihar a yau, rundunar 'Yan sandan Jihar ta yi kira ga al'umma da su gujewa dukkan abun da zai janyo rikici ko hayaniya a dukkan sassan Jihar. Kakakin Rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya faɗi haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis inda ya ce haƙƙin hukumarsu ne su kula da rayuka da dokiyoyin al'ummar Jihar, dan haka kar su amincewa duk wani yunƙuri na tada-zaune-tsaye a lokacin gudanar da shari'ar ko bayan haka. A…
Read More

Gwamnan Ribas ya rantsar da kwamitin riƙon ƙwarya ga ƙananan hukumomin Jihar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya naɗa kwamitin riƙon ƙwarya ga dukkan ƙananan hukumomin Jihar guda 23 sakamakon rikicin zaɓe dake gudana a faɗin Jihar. An gudanar da taron rantsarwar ne a ranar Laraba a fadar gwamnatin Jihar dake Fatakwal, babban birnin Jihar, domin kawo ƙarshen tashin-tashina a sassa daban-daban na Jihar. Gidan talabijin na 'channels', ya ruwaito cewa, sai da gwamnan ya miƙa sunayen mutanen ga Majalisar dokokin Jihar domin tantancewa wanda bayan haka ne suka amince da hukuncin gwamnan. Haka nan, naɗin ƴan riƙon ƙwaryar ya faru ne sakamakon miƙa ƙudurin ƙara wa'adin shugabancin…
Read More

A guji ajiye abinci a firji fiye da kwana uku – NAFDAC

Daga ABUBAKAR SULAIMAN Darakta Janar ta hukumar kula da abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC), Farfesa Moji Adeyeye, ta shawarci ƴan Najeriya da su guji ajiye dafaffen abinci a firji na tsawon fiye da kwanaki uku saboda haɗarin kamuwa da cutuka. Sanarwar ta fito ne daga mai bada shawara kan harkokin yaɗa labarai na hukumar, Sayo Akintola a ranar kiyaye abinci ta duniya ta shekarar 2024. Adeyeye, ta bayyana muhimmancin kiwon lafiyar jama’a da tattalin arziƙi dake tattare da rashin tsaftataccen abinci, inda ta ce kusan mutane miliyan 600 ne a faɗin duniya ke fama da rashin lafiya a duk…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta haƙiƙance kan biyan naira dubu 62 mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ce naira dubu 250 da hukumar ƙwadago suka buƙaci ta ke biya a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata abu ne mai nauyi a gareta inda take ganin adadin ya yi yawan da ba zata iya kikayewa ba. Gwamnatin ta yi sanarwar ne ta ofishin mai taimakawa Shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga a ranar Lahadi biyo bayan nuna damuwa da ƙungiyar ƙananan hukumomin Najeriya ta yi kan naira dubu 62 da gwamnatin ta sanar zata ke biya a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan ƙasar. A ranar 28 ga…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata sauya sunan hanyar Murtala Mohammed dake Abuja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar cewa ta canja sunan hanyar Murtala Mohammed dake Abuja zuwa Wole Soyinka. Wata sanarwa da mai taimaka wa ministan harkokin yaɗa labarai da haɗin kan 'yan ƙasa, Rabi'u Ibrahim ya fitar ranar Litinin, ta ce gwamnatin Shugaba Tinubu bata taɓa yunƙurin sauya sunan hanyar ba. A ƴan kwanakin nan ne aka samu jita-jitar sakamakon buɗe wata sabuwar hanya da gwamnatin tayi wacce ke daga Katampe zuwa Jahi inda ministan Abuja, Barista Nyesom Wike ya shawarci shugaba Tinubu da a sa sunan Wole Soyinka wa hanyar, kuma ya amince da hakan. Sanarwar…
Read More