A guji ajiye abinci a firji fiye da kwana uku – NAFDAC

Daga ABUBAKAR SULAIMAN

Darakta Janar ta hukumar kula da abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC), Farfesa Moji Adeyeye, ta shawarci ƴan Najeriya da su guji ajiye dafaffen abinci a firji na tsawon fiye da kwanaki uku saboda haɗarin kamuwa da cutuka.

Sanarwar ta fito ne daga mai bada shawara kan harkokin yaɗa labarai na hukumar, Sayo Akintola a ranar kiyaye abinci ta duniya ta shekarar 2024.

Adeyeye, ta bayyana muhimmancin kiwon lafiyar jama’a da tattalin arziƙi dake tattare da rashin tsaftataccen abinci, inda ta ce kusan mutane miliyan 600 ne a faɗin duniya ke fama da rashin lafiya a duk shekara sakamakon amfani da gurbataccen abinci, yayin da kusan 420,000 ke mutuwa.

Jaridar ‘Leadership Hausa’, ta ruwaito cewa, an ƙiyasta nauyin tattalin arzikin duniya na ayyukan abinci marasa aminci da dala biliyan 110 a kowace shekara wanda galibi suna shafar ƙasashen da ba su ci gaba ba, da masu tasowa ta hanyar asarar kayan aiki da kuma kashe kuɗin magani.

Farfesar, ta ƙara da cewa, kiyaye abinci yana da muhimmanci ba kawai ga lafiyar jama’a ba, har ma da ci gaban tattalin arziƙi da kuma samar da wadataccen abinci ga al’umma.