Mahaifiyar Bukola Saraki ta rasu

Allah yayi wa mahaifiyar Abubakar Bukola Saraki, MADAM Florence Morenike Saraki rasuwa.

Jaridar daily trust ta rawaito, mahaifiyar mai shekaru 88 ta yi doguwar suma kafin a kai ta asibiti a jihar Legas.

Wata majiya na cewa, abun ya faru ne da yammacin yau lokacin da mama tai doguwar suma, a ka dauketa a ka tafi da ita asibiti, wanda daga bisani a ka kwantar da ita a dakin jinyar masu kula ta musamman.

Marigayiyar, ta kasance mata ga tsohon sanatan jamhuriya ta biyu Olusola Saraki, wanda shine jagoran siyasar jihar Kwara kafin Rasuwar shi a shekarar 2012.