An yi garkuwa da mai naƙuda akan hanyarta ta zuwa asibiti

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wata mata mai juna biyu dake gaf da haihuwa a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Lamarin ya faru ne da matar mai suna Ogunbunmi, a unguwar Oke Lantoro akan hanyarta ta zuwa asibiti a ranar Alhamis.

Mijinta mai suna Mista Lateef Ogunbunmi ya ce ya ga saƙo ta ‘wattsapp’ cewa an yi garkuwa da matarsa daga waɗanda suka yi garkuwar da ita.

Kakakin Rundunar Ƴan sandan yankin, Omolola Odutola ya tabbatar da labarin a lokacin da mijin matar ya shigar da ƙara a babban ofishinsu dake yankin Kemya inda mijin ya ce matarsa mai shekaru 32 wacce ke gaf da haihuwa ta bar gida tun misalin ƙarfe 10:30 na safe, basu ji labarinta ba sai dai kawai ya ga saƙon aukuwar lamarin.

An kuma samu rahoton cewa, ƴan bindigar sun kasance ɗauke da bindigu da wuƙaƙe sannan kuma sai da suka sauya mata mota a yayin al’amarin.

By Babaji