‘Yan sanda sun ƙwato shanu 20 daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Yan sandan Katsina sun daƙile wani yunƙurin satar shanu a ƙaramar hukumar Jibia, inda suka yi nasarar ƙwato shanu 20 daga hannun ‘yan bindigan bayan musayar wuta.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar da takardar sanarwa inda ya bayyana cewa lokacin da (DPO) ya samu kiran gaggawa cewa wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Korama Mai Zurfi har sun sace shanu 20.

Bayan samun rahoton, DPO ya gaggauta tura jami’an sashen yaƙi da manyan laifuka (VCRU) tare da haɗin gwiwar jami’an sa-kai zuwa wurin da lamarin ya faru. Jami’an tsaron sun tare hanyoyin da ‘yan bindigar za su bi wajen tserewa, lamarin da ya haifar da musayar wuta mai zafi.

DSP Sadiq ya ce jami’an su sun sami galaba a kan ‘yan bindigar sakamakon amfani da ingantattun dabarun yaƙi da kuma ƙarfin makamai. Ya ce hakan ya tilasta wa maharan barin dukkan shanun da suka sace tare da tserewa cikin daji ɗauke da raunukan harbin bindiga daban-daban.

An yi nasarar ƙwato dukkan shanun 20 da aka sace, yayin da jami’an tsaro suka ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin. Haka kuma, rundunar ta ce ana ci gaba da farautar waɗanda suka tsere domin cafke su.

Kwamishinan ‘yan wandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya yabawa jami’an rundunar da kuma jami’an sa-kai kan saurin ɗaukar mataki, jarumtaka da haɗin gwiwar da suka nuna yayin gudanar da aikin. Ya sake jaddada ƙudirin rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.

Rundunar ta kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar ba su sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimakawa wajen yaƙi da laifuffuka. Ta tabbatar da cewa duk bayanan da jama’a suka bayar za a kula da su cikin cikakkiyar sirri.

By ukarofi

Leave a Reply