Jami’an kwastom 1,516 za su yi ritaya cikin shekaru biyu – NCS

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) ta fitar da jerin jami’anta da za su yi ritaya a shekarun 2026 da 2027, inda jimillar jami’ai 1,516 za su bar aiki bisa tanadin dokokin aikin gwamnati ƙasar.

Bayanan sun nuna cewa jami’ai 825 za su yi ritaya a shekarar 2026, yayin da wasu 691 za su yi ritaya a shekarar 2027. Wannan na daga cikin mafi girman adadin jami’an da za su fice daga aikin hukumar a lokaci guda a tarihin ta na baya-bayan nan.

Takardun sanarwar ritayar, waɗanda Sashen Kula da Harkokin Ma’aikata da Ci Gabansu na Hukumar Kwastom ya fitar, sun nuna cewa ritayar ta shafi kusan dukkan matakan muƙamai, daga Mataimakin Kwanturola-Janar na Kwastam har zuwa Mataimakin Jami’in Kwastam na Mataki na Biyu.

Takardun, waɗanda Kwanturola mai kula da harkokin ma’aikata, A.A. Bazuaye, ya sanya wa hannu a madadin Mataimakin Kwanturola-Janar mai kula da harkokin ma’aikata da ci gaba, sun ce an shirya ritayar ne bisa ƙa’idojin Dokokin Aikin Gwamnati.

Jerin ritayar shekarar 2026 ya ƙunshi jami’ai 825. A cikin su, mafi yawan waɗanda abin ya shafa suna matakin Mataimakin Sufurintandan Kwastom, su 285, sai kuma Sufurintandan Kwastom guda 226.

Sauran sun haɗa da Mataimakin Sufurintanda na Farko, Manyan Jami’an Kwastom, Mataimakan Jami’an Kwastom, Babban Sufurintandan Kwastom, da wasu manyan jami’ai har da Mataimakan Kwanturola-Janar da Mataimakan Kwanturola-Janar na ƙasa.

A shekarar 2027 kuwa, jami’ai 691 ne ke cikin jerin ritayar. Sufurintandan Kwastom ne suka fi yawa da mutum 200, sai Mataimakan Sufurintandan Kwastam guda 193.

Jerin ya kuma haɗa da manyan jami’ai daga matakai daban-daban, ciki har da Mataimakan Kwanturola-Janar guda huɗu.

Hukumar ta umarci dukkan jami’an da abin ya shafa da su fara hutun watanni uku kafin ranar ritayarsu, kamar yadda Dokokin Aikin Gwamnati suka tanada.

Haka kuma an umurce su da su aika da takardar sanarwar ritaya zuwa ofishin Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastom.

A sanarwar, hukumar ta ce duk wani kuskure ko ƙorafi da aka gano cikin jerin ritayar shekarar 2027 ya kamata a aika zuwa ofishin Mataimakin Kwanturola-Janar mai kula da harkokin ma’aikata kafin ranar 31 ga Yulin 2026.

Shugaban Kwamitin Kwastom da Haraji na Majalisar Wakilai, Hon. Abejide Leke Joseph, ya bayyana cewa ritayar ba ta da alaƙa da raɗe-raɗin da ake yi kan naɗin sabon Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastom.

Ya ce dokokin aikin gwamnati sun tanadi ritaya bayan shekaru 35 na aiki ko kuma kai shekaru 60 da haihuwa, don haka babu wanda ake korar sa domin ba wa wani gurbi.

A cewarsa, yawan jami’an da za su yi ritaya ya samo asali ne daga dogon lokacin da ba a ɗauki sabbin ma’aikata ba a hukumar, lamarin da ya sa jami’ai masu lambobin aiki iri ɗaya suka yi girma tare kuma suka kai matsayin manyan jami’ai a lokaci guda.

Ya ƙara da cewa, wannan ya haifar da yanayin da jami’ai da dama suka kai shekarun ritaya ko iyakar shekarun aiki a lokaci guda.

Wannan ci gaba na zuwa ne bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin wa’adin watanni shida ga Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastom, Adewale Adeniyi.

Sanarwar da Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce ƙarin wa’adin zai ba Adeniyi damar kammala muhimman gyare-gyaren da ake aiwatarwa a hukumar.

A cewar sanarwar, za a yi amfani da lokacin wajen ƙarfafa aiwatar da tsarin National Single Window da kuma tabbatar da miƙa ragamar shugabanci cikin tsari da lumana.

By ukarofi

Leave a Reply