Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya naɗa sabbin masu sarauta a Masarautar Kano, ciki har da Alhaji Muhammadu ɗan’iya Ibrahim a matsayin Kachallan Kano, Alhaji Sa’adu Ali Ibrahim Matawalle a matsayin Mayanan Kano, da kuma Alhaji Sa’adu Giɗaɗo a matsayin Sarkin Arewan Kano.
An gudanar da bikin naɗin sarautun ne a Fadar Sarkin Kano a ranar Juma’ar da ta gabata, inda aka halarta daga sassa daban-daban na jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Da yake jawabi bayan naɗin nasa, sabon Kachallan Kano, Alhaji Muhammadu Daniya Ibrahim, ya bayyana farin cikinsa tare da godiya ga Allah da kuma Sarkin Kano bisa wannan karramawa da aka yi masa.
Ya ce ɗaukaka shi zuwa matsayin Kachallan Kano babban abin alfahari ne a rayuwarsa, yana mai alƙawarin yin aiki tukuru domin ci gaban Masarautar Kano da al’ummar jihar baki ɗaya.
“Zan yi duk abin da zan iya wajen kare martabar Masarautar Kano da kuma tallafa wa ayyukan da za su amfani al’umma,” inji shi.
Haka kuma ya yaba da ƙoƙarin Sarkin Kano da Gwamnan Jihar Kano wajen haɗa kan al’umma da inganta zaman lafiya a jihar.
A nasa ɓangaren, sabon Sarkin Arewan Kano, Alhaji Sa’adu Giɗaɗo, ya bayyana cewa sarautarsa ita ce ta farko irinta a tarihin Masarautar Kano.
Ya ce ko da yake a baya akwai wakilan yankuna daban-daban kamar na Gabas, Yamma, Kudu da Arewa, amma sarautar Sarkin Arewan Kano sabuwa ce da aka kirkiro domin ƙara bunƙasa tsarin sarautun gargajiya.
Ya yaba wa Sarkin Kano bisa hangen nesa da ƙoƙarin da yake yi na farfaɗo da tarihi da kuma bai wa gidajen sarauta damar taka rawar gani a harkokin masarauta.
Ita ma Dr. Asma’u Baba Ibrahim ɗanbappa, matar Mayanan Kano, ta nuna farin cikinta da naɗin da aka yi wa mijinta, tana mai cewa wannan babban abin alfahari ne ga iyali da zuriyarsu baki ɗaya.
Ta yabawa Sarkin Kano bisa yadda yake karrama mutane da kuma ƙarfafa alaƙa tsakanin masarauta da al’umma.
A nata jawabin, Hajiya Zainab Matawalle ta ce suna ci gaba da yi wa Sarkin Kano addu’ar Allah Ya ba shi nasara wajen gudanar da harkokin masarautar tare da cika manufofin da ya sanya a gaba.
