Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Yayin da gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke cika shekaru uku a mulki, shugabannin wasu manyan kasuwanni a jihar sun bayyana buƙatunsu tare da neman ƙarin tallafi daga gwamnati domin magance matsalolin da suke fuskanta.
Kasuwannin da suka bayyana damuwarsu sun haɗa da Kasuwar Kurmi, Kasuwar Abba Tuwa da kuma Kasuwar Gidan Bos, waɗanda ke daga cikin muhimman cibiyoyin kasuwanci a jihar Kano.
Da yake zantawa da wakilinmu, Shugaban ƙungiyar ’Yan Kasuwar Kurmi, Alhaji Sulaiman Umar Sanka, ya ce duk da irin ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ke yi, har yanzu kasuwar na buƙatar kulawa ta musamman.
Ya bayyana cewa akwai sama da ƙofofi 130 da ke buƙatar gyara, tare da buƙatar inganta magudanan ruwa, samar da hasken wuta da kuma cika wasu alkawuran da gwamnati ta yi wa kasuwar.
A cewarsa, duk da cewa sun gabatar da bukatunsu ga gwamnatin jihar, har yanzu ba su samu tallafin da suke fata ba.
“Mun gana da gwamna kuma mun gabatar masa da matsalolinmu, amma har yanzu ba mu samu wani tallafi kai tsaye ba,” inji shi.
A nasa ɓangaren, Sakataren Kuɗi na ƙungiyar Mahautan Kano, Alhaji Basiru Abdullahi Kata, ya ce mahautan jihar sun taɓa samun tallafi mai yawa daga gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso tsakanin shekarun 2011 zuwa 2015, ciki har da tallafin jari da motocin ɗaukar nama.
Ya ce tun bayan wannan lokaci ba su sake samun wani tallafi mai kama da wanda aka ba su a wancan lokacin ba.
Sai dai ya bayyana cewa har yanzu suna da kyakkyawan fata kan gwamnatin Abba Kabir Yusuf kuma suna sa ran za ta dubi bukatunsu nan gaba.
Haka kuma, Shugaban ƙungiyar ’Yan Kasuwar Gidan Bos, Alhaji Idris Shukuriya, ya yabawa gwamnatin jihar kan ayyukan gine-ginen tituna da haskaka wasu sassa na Kano.
Sai dai ya ce kasuwar Gidan Bos na fuskantar matsalar rashin isasshen hasken wutar lantarki, musamman a cikin kasuwar.
Ya bayyana cewa kasuwar tana samar wa dubban matasa ayyukan yi, don haka akwai buƙatar gwamnati ta taimaka wajen samar da fitilun titi da sauran kayan more rayuwa domin ƙarfafa tsaro da bunƙasa harkokin kasuwanci.
Ya ƙara da cewa ’yan kasuwar a shirye suke su bayar da tasu gudunmawa idan gwamnati ta nuna aniyar haɗin gwiwa wajen magance matsalolin da suke fuskanta.
Shugabannin kasuwannin sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara mayar da hankali kan buƙatun ’yan kasuwa, suna masu cewa bunƙasa kasuwanni na daga cikin hanyoyin ƙarfafa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa a jihar.
.
