Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shirya gurfanar da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin badakalar kuɗi da kuma tallafa wa ayyukan ta’addanci.
Jaridar Punch ta rawaito cewa, EFCC ta shigar da tuhume-tuhume guda 12 a kansa, inda ta zarge shi da karɓar kuɗaɗen dala har miliyan 2.53 ta Amurka da ake zargin sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka.
A cewar hukumar, Bodejo ya karɓi kuɗaɗe daga tsohon Akanta Janar na Jihar Bauchi, Sa’idu Abubakar, ba tare da an bi ta hanyoyin bankuna ba kamar yadda doka ta tanada.
Daga cikin zarge-zargen, EFCC ta ce Bodejo ya karɓi dala 100,000 a watan Janairun 2022, sannan daga baya ya sake karɓar dala 200,000 daga mutum guda.
Haka kuma, ana zarginsa da karɓar dala 980,000 a watan Fabrairun 2024 da kuma dala 500,000 a watan Maris na shekarar 2024, duk a tsabar kuɗi ba tare da bin hanyoyin da doka ta tanada ba.
Hukumar ta kuma ce Bodejo ya mallaki wasu kuɗaɗe da ake zargin sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka, lamarin da ya sa ake zarginsa da laifukan badakalar kuɗi.
Ana sa ran za a gurfanar da shi a kotu da zarar an sanya ranar sauraron karar.
