Kofin Duniya: Ecuador ta tsallake zuwa zagayen ‘yan 32 bayan doke Jamus

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A cigaba da fafatawa a gasar Kofin Duniya na 2026, ƙasar Ecuador ta yi nasarar hayewa zuwa zagayen ‘yan 32 bayan doke Jamus da ci 2 da 1 a wasan ƙarshe na rukunin E a ranar Alhamis.

Ita ma Jamus, wadda ta lashe kofin har sau huɗu a tarihinta, ta tsallake zuwa zagayen bayan samun nasara a wasa biyun farko.

Lorey Sane na Jamus ne ya fara zura ƙwallo a ragar Ecuador a zangon farko na wasan, inda daga bisani ƙasar Nahiyar Amurkan ta farke da kuma ƙara ƙwallo ta biyu a raga.

Wannan al’amari ya sa ta tsallake zuwa zagaye na gaba a gasar da maki shida sakamakon yawan ƙwallaye da ta fi Cote d’Ivoire da su.

By Babaji

Leave a Reply