Yadda gwamnoni ke shiriritar da fafutukar Tinubu ta ’yancin ƙananan hukumomi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A watan Yuli na shekara ta 2024 Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya samu gagarumar nasara a fafutukar da ya yi na ganin ƙananan hukumomin ƙasar sun samu cikakken ’yancin cin gassin kansu, musamman ta fuskar kuɗaɗen shiga, lamarin da manazarta ke dangantawa da yadda gwamnonin ƙasar ke neman shiriritar da batun.

Duk da cewa Kotun ƙolin Nijeriya ta yanke wannan muhimmin hukunci a shekarar 2024, wanda ya bai wa ƙananan hukumomi 774 na ƙasar cikakken ikon karɓar kuɗaɗensu kai tsaye daga Asusun Tarayya, har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta iya aiwatar da hukuncin ba, lamarin da ya ci gaba da haifar da cece-kuce kan makomar mulkin ƙananan hukumomi a ƙasar.

Tun daga lokacin da kotun ta yanke hukuncin, masu sharhi da masana harkokin mulki sun yi amannar cewa matakin zai zama babban juyin juya hali wajen ƙarfafa ƙananan hukumomi, domin su samu damar gudanar da ayyukan raya karkara ba tare da katsalandan daga gwamnatocin jihohi ba. Sai dai kusan shekaru biyu bayan haka, har yanzu tsarin da aka saba amfani da shi na raba kuɗaɗen ƙananan hukumomi ta hannun jihohi sam bai sauya ba.

Lamarin ya samo asali ne bayan Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya shigar da ƙara a gaban Kotun ƙoli kan gwamnonin jihohi 36 da manyan lauyoyinsu, yana neman a tabbatar da cikakken ’yancin kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Gwamnatin tarayya ta zargi gwamnatocin jihohi da riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi tare da sakin su a hankali, abin da ta ce ya raunana ayyukan hukumomin a matakin karkara.

A ranar 11 ga Yulin 2024, Kotun ƙoli ta yanke hukunci mai tarihi inda ta amince da buƙatun gwamnatin tarayya. Mai shari’a Emmanuel Agim, wanda ya karanta hukuncin kotun, ya bayyana cewa ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki gwamnoni su ci gaba da karɓar kuɗaɗen ƙananan hukumomi ko kuma su riƙe su.

Kotun ta umarci cewa daga wannan lokaci, kuɗaɗen da aka ware wa ƙananan hukumomi daga Asusun Tarayya su riƙa shiga kai tsaye cikin asusun ƙananan hukumomin.

Baya ga batun kuɗi, kotun ta kuma hana gwamnoni rusa zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi tare da maye gurbinsu da kwamitocin riƙon ƙwarya, wata dabara da aka daɗe ana amfani da ita a wasu jihohi.

A lokacin, masana harkokin shari’a sun yaba da hukuncin, suna masu cewa zai ƙarfafa tsarin rabon iko da kuma ba ƙananan hukumomi damar gudanar da harkokinsu cikin ’yanci.

Sai dai farin cikin ya fara dusashewa yayin da aiwatar da hukuncin ya fuskanci cikas.

Binciken da aka gudanar bayan shekara guda da hukuncin ya nuna cewa gwamnonin jihohi sun ci gaba da sarrafa kuɗaɗen ƙananan hukumomi, duk da cewa adadin kuɗin da ya kai kusan naira tiriliyan 4.5 ya kamata ya riƙa shiga kai tsaye ga ƙananan hukumomin.

Ko da yake gwamnatin tarayya ta umarci Babban Bankin Nijeriya da ya buɗe asusun banki na musamman ga kowace ƙaramar hukuma domin sauƙaƙa biyan kuɗaɗen kai tsaye, har yanzu kuɗaɗen na ci gaba da bi ta hannun gwamnatocin jihohi.

A wasu jihohi ma, an ɗauki matakan doka da suka saɓa da ruhin hukuncin Kotun ƙoli. Misali, Majalisar Dokokin Jihar Anambra ta amince da wata sabuwar doka da ta tanadi cewa kuɗaɗen ƙananan hukumomi za su ci gaba da shiga cikin Asusun Haɗin Gwiwa na Jiha da ƙananan Hukumomi. Gwamnan jihar, Chukwuma Soludo, ya kare matakin yana mai cewa zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya da daidaito wajen tafiyar da kuɗaɗen. Sai dai masana sun ce wannan mataki ya yi karo kai tsaye da hukuncin Kotun ƙoli.

A wani ɓangaren kuma, Jihar Nasarawa ta gyara dokokinta domin dacewa da hukuncin kotun, inda ta soke tsarin asusun haɗin gwiwa gaba ɗaya.

Duk da gargaɗin da Babban Lauyan Tarayya ya yi wa gwamnonin da suka ƙi bin hukuncin kotu, ciki har da barazanar gurfanar da su kan raina kotu, har yanzu babu wani gwamna da aka ɗauka wa matakin ladabtarwa.

Wata majiya daga ofishin Babban Lauyan Tarayya ta bayyana cewa ofishin ba shi ne ke kula da rabon kuɗaɗe kai tsaye ba, lamarin da ke nuna yadda aiwatar da hukuncin ya makale tsakanin hukumomi daban-daban.

Rahotanni sun nuna cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya saurari koke-koken gwamnoni kan lamarin tare da ɗora wa Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, da Babban Lauyan Tarayya alhakin warware matsalolin da ke hana aiwatar da hukuncin.

Sai dai har yanzu babu wani tsayayyen tsarin da ya tabbatar da fara biyan kuɗaɗen kai tsaye ga ƙananan hukumomi.

ƙungiyoyin ƙwadago ma sun fara nuna rashin jin daɗi kan yadda lamarin ke tafiya. Shugaban ƙungiyar Kwadago na Jihar Gombe, Yusuf Bello, ya bayyana cewa babu wani gagarumin sauyi da aka samu tun bayan hukuncin, yana mai cewa har yanzu shugabannin ƙananan hukumomi ba su da cikakken iko a kan kuɗaɗensu.

Duk da cewa kuɗaɗen ƙananan hukumomi na ci gaba da karuwa a rabon kuɗaɗen tarayya na wata-wata, matsalar da ke ci gaba da addabar tsarin ita ce hanyar da kuɗin ke bi kafin su isa ga hukumomin. Masana sun ce, gwamnoni na ci gaba da adawa da tsarin ne saboda dalilai uku masu muhimmanci.

Na farko shine, siyasar rabon gata da albarkatu, domin kuɗaɗen ƙananan hukumomi sun kasance wata muhimmiyar hanya da wasu gwamnoni ke amfani da ita wajen kula da magoya baya da sauran jiga-jigan siyasa.

Na biyu kuwa shine tsoron cewa idan shugabannin ƙananan hukumomi suka samu cikakken ikon kuɗaɗensu, za su iya zama wata sabuwar cibiyar siyasa da za ta ƙalubalanci ikon gwamnoni a jihohinsu.

Na uku kuma shine batun kuɗaɗen shiga na cikin gida, inda wasu jihohi ke ci gaba da riƙe kaso da ya kamata a bai wa ƙananan hukumomi.

Masana harkokin mulki sun yi gargaɗin cewa muddin ba a gyara Kundin Tsarin Mulki ba, za a ci gaba da samun giɓi a aiwatar da hukuncin.

Sun nuna cewa sashe na 162(6) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 har yanzu yana tanadar da Asusun Haɗin Gwiwa tsakanin jihohi da ƙananan hukumomi, abin da ke ba wa gwamnatocin jihohi hujjar ci gaba da jinkirta aiwatar da hukuncin.

Duk da cewa Majalisar Tarayya ta nuna goyon baya ga hukuncin Kotun ƙoli tare da bayyana aniyarta ta yi gyaran Kundin Tsarin Mulki domin tabbatar da cikakken aiwatar da shi, har yanzu babu wani gyara da aka yi a hukumance.

Masu fafutukar tabbatar da kyakkyawan shugabanci sun ce lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta daina sasanci da gwamnoni ta koma aiwatar da hukuncin kotu kai tsaye.

A cewarsu, idan ƙananan hukumomi suka samu cikakken ikon kuɗaɗensu, za a fara ganin sauye-sauye kai tsaye a rayuwar al’umma ta hanyar biyan albashi da fansho a kan lokaci, gyaran hanyoyin karkara, da kuma inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.

Yayin da ake ci gaba da jiran matakin gwamnati, har yanzu akwai babban gibi tsakanin abin da Kotun ƙoli ta umarta da kuma abin da ke faruwa a zahiri a ƙananan hukumomi 774 na Nijeriya.

Da aka nemi jin ta bakin mai taimaka wa Babban Lauyan Tarayya kan harkokin yaɗa labarai, Kamarudeen Ogundele, ya bayyana cewa kwamitin da Sakataren Gwamnatin Tarayya ke jagoranta ne ke kula da aiwatar da hukuncin.

Sai dai mai taimaka wa George Akume kan harkokin yaɗa labarai, Yomi Odunuga, bai bayar da cikakken bayani kan matakin da aka kai wajen aiwatar da hukuncin ba.

By ukarofi

Leave a Reply