Gwamnatin Katsina ta bada aikin gina cibiyar samar da ruwan sha 66

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

A ƙoƙarin ta na wadata al’ummar jihar da ruwan sha, gwamnatin jihar Katsina ta bada aikin gina cibiyar samar da da ruwan sha ƙarƙashin shirin (Small Town Water Supply) STOWSSA guda 66 a wasu sassan jihar.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanar da haka a lokacin da yake ƙaddamar da ɗaya daga cikin cibiyar samar da ruwan sha a garin Tsagero, ƙaramar hukumar Rimi.

Ya ce garuruwar da suka amfana da shirin sun haɗa da Katsina, Funtua,Baure,Kankara, Ƙafur, Daura, Charanchi,Batagarawa, Matazu da Faskari.

Haka kuma Dikko Raɗɗa ya faɗa cewa gwamnatin sa ta samar da lita 30,000 na ruwan sha a kowace cibiyar bayar da ruwan sha bayan kowace awa guda tare da gina magewayi mai ɗauke da fitilla mai amfani da hasken rana da busashe guda 500.

Gwamna ya bayyana cewa yanzu haka an kammala gina 32 na irin waɗannan cibiyoyi, sauran wasu sun fara samar da ruwan sha wasu kuma an kammala ana kiran ƙaddamar wa.

Malam Dikko Raɗɗa ya ce irin wannan da wasu nasarorin da gwamnatin sa ta samu ya nuna tashi tsaye da aka yi wajen kawo ƙarshen matsalar ruwan sha a faɗin jihar.

Ya ce yanzu haka gwamnati na gudanar da wasu aikace aikace da zai inganta samar da wadataccen ruwan sha a faɗin jihar da suka haɗa da sayen man dizel da magungunan tsabace ruwan sha da gwamnati ke samarwa a kowanne wata.

Akwai aikin samar da ruwan sha na Zobe Dam kashi na biyu wanda da zaran an kammala zai wadata ƙananan hukumomin da ke kewaye da madatsar ruwa da sauran wasu aikace aikace kamar yadda gwamnan ya ce.

Gwamnan sai yayi kira da shugabannin alumma na waɗannan yankuna da suka amfana da su riƙa sa ido saboda ɓatagari.

By ukarofi

Leave a Reply