CBN ya umarci a riƙe asusun da aka alaƙanta da ayyukan ta’addanci a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Bankin Nijeriya CBN, ya umarci dukkan bankuna da cibiyoyin kuɗi a Nijeriya da su gaggauta riƙe asusu da kadarorin da aka danganta su da mutane shida da wasu ma’aikatan kasuwar canji (BDC) su huɗu bisa zargin su da ɗaukar nauyin ta’addanci.

A ranar 24 ga Yuni, 2026 ne bankin ya fitar da umarnin a takarda mai ɗauke da lamba kamar haka: Ref: CMD/FCS/PUB/CIR/002/011, inda ya ce za a fara aiwatar umarnin ne akan jaddawalin waɗanda gwamnatin Nijeriya ta fitar da sunayensu akan batun hannu a ta’addanci.

CBN ya ce, yana sanar da cibiyoyin kuɗaɗen game da sababbin hukunce-hukuncen daga Kwamitin Hukunce-hukuncen na Ƙasa (NIGSAC) da Sashen Gudanarwar Kadarorin Waje na Ma’aikatar Asusun Ƙasa na Amurka (OFAC) ya yi akansu a ƙarƙashin dokar ƙasa.

Mutane shidan da aka sanya su a jaddawalin masu takunkumin na SDN da Blocked Persons List sune Muktar Muhammad Adamu, Babangida Muhammed Adamu Hammajam, Abdullahi Umar Usman, Ibrahim Abubakar, Adamu Chiroma, da Yakubu Ogirima Ibrahim.

Haka kuma, akwai cibiyoyin kuɗi na Nijeriya da na ‘yan BDC huɗu da mutanen ke gudanarwa da suka haɗa da: Generation Currency Bureau De Change Limited, Manhattan Bureau De Change Limited, Nine to Nine Exchange Bureau De Change Limited, da kuma Abbal Bako & Sons Bureau De Change Limited.

Wannan umarni na zuwa ne bayan da Amurka ta sanya takunkumi akan Mukhtar Muhammad, wanda ɗan harkar canji ne mazaunin Legas da wasu kamfanoni huɗu da ke ƙarƙashin ikonsa.

A wata sanarwa da OFAC ta fitar a mako guda da ya gabata, ta zargi Muhammad wanda aka sani da Mukhtar Adamu Muhammad da shirya hada-hadar kuɗaɗe a madadin ƙungiyar Islamic State West Africa Province, wato ISWAP.

Haka kuma, OFAC ta zayyano kamfanonin Nine To Nine Exchange Bureau De Change Limited, Generation Currency Bureau De Change Limited, da Manhattan Bureau De Change Limited, a jaddawalin nata, inda ta zarge su da cewa ana amfani da su wajen tafiyar da harkokin kuɗaɗen ƙungiyar ta’addancin.

Kazalika, CBN ya gargaɗi cibiyoyin da su tabbatar da cewa babu wani kuɗi, ko hidimar kuɗaɗe ko albarkatun tattali da aka samar kai tsaye ko a fakaice ga mutanen da kamfanonin da aka danganta da su.

By Babaji

Leave a Reply