
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Aƙalla mutane 164 ne suka rasa rayukansu yayin da 971 suka jikkata a sakamakon iftila’in girgizar ƙasa guda biyu da ya auku a ƙasar Venezuela, lamarin da ya haifar da rushewar gine-gine da tilasta wa hukumomin tsaro ayyana dokar ta-ɓaci.
Shugabar riƙo ta ƙasar, Delcy Rodriguez ta ce al’amarin ya auku ne a cikin daƙiƙa 40 a ranar Laraba da dare.
Wannan girgizar ƙasa ita ce mafi muni a tsawon sama da shekara 100 da ta samu ƙasar kudancin Amurkan, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Yankin La Guaira, wato arewacin babban birnin ƙasar Caracas ne ya fi gamuwa da munin iftila’in musamman ganin yadda ya yi damejin kaso mai girma, saboda haka hukumomi suka ayyana shi a matsayin mafi haɗarin yanki.
Tuni dai jami’an ceto suka cigaba da binciken buraguzan gine-ginen da suka rufta da ƙoƙarin ceto waɗanda suka tsira da kuma zaƙulo gawarwaki, inda suka yi gargaɗin cewa adadin waɗanda suka rasu ka iya ƙaruwa.
Haka kuma, an dakatar da harkoki da dama ciki har da rufe babban filin jiragen saman ƙasar da zirga-zirgar jiragen ƙasa da dai sauransu.
Akan haka ne Rodriguez ta sanar da shirin gwamnatinsu na tallafa wa yankunan da iftila’in ya afka wa da kuma ɗaukar matakan bayar da agajin gaggawa.

