Daga UMAR GARBA a Katsina
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi watsi da wani bidiyo da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta inda aka ga wasu jami’an ‘yan sanda suna mu’amala da ɓarayin daji a jihar Katsina, rundunar ta bayyana labarin a matsayin ƙarya da kuma yaudara.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da Jama’a na rundunar, CSP Anietie Okokon Edem Iniedu ya fitar a ranar Laraba, ‘yan sandan sun ce mutanen da aka gani a cikin bidiyon ba ‘yan bindiga ba ne, mambobin ƙungiyar Vigilante Group of Nigeria (‘yan banga) da kuma mafarauta masu rijista waɗanda ke taimaka wa hukumomin tsaro a ayyukan da ake gudanarwa na samar da tsaro a jihar Katsina.
A cewar ‘yan sanda, an ɗauki bidiyon ne a yayin da ‘yan bangar ke kan hanyarsu ta zuwa wani aikín tsaro don tallafa wa wajen yaƙi da laifuka da inganta tsaron jama’a a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu na jihar.
“Domin guje wa shakku, mutanen da aka nuna a bidiyon ba ‘yan fashi ba ne. Su membobin ƙungiyar Vigilante Group of Nigeria (VGN) ne da aka amince da su da kuma mafarauta da aka yi wa rijista waɗanda ke tallafa wa ayyukan tsaro da ake gudanarwa tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu na Jihar Katsina,” in ji sanarwar.
Rundunar ta dage cewa zarge-zargen da ke nuna cewa wani jami’in ɗan sanda yana hulɗa da ‘yan bindiga “ƙarya ne kawai, mugunta ne, kuma an yi haka ne don rikita jama’a.”
Sanarwar ta ce ‘yan sanda sun yi Alla- wadai da abin da suka bayyana a matsayin karkatar da gaskiya da gangan da kuma yaɗa labaran ƙarya waɗanda za su iya haifar da fargaba ga jama’a, da kuma lalata amincewa da cibiyoyin tsaro da kuma lalata ayyukan tsaro da ake gudanarwa.
Ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da zarge-zargen da aka yi sakamakon ɓullar bidiyon, rundunar ta kuma buƙaci jama’a da su dogara ne kawai da bayanan da aka fitar ta hanyoyin hukumar ‘yan sanda da sauran majiyoyin gwamnati.
Rundunar ta kuma yi gargaɗi ga mutane da kafafen yaɗa labarai da ke da hannu a ƙirƙira ko yaɗa labaran ƙarya waɗanda za su iya barazana ga zaman lafiyar jama’a da tsaro, inda ta ce za a iya ɗaukar matakin shari’a a kan masu laifi.
Bidiyon wanda yanzu haka ke yawo a shafukan sada zumunta an nuna wasu mutane masu tarin yawa, saman babura, ɗauke da muggan makamai suna wucewa kan hanya a wajen wani shingen binciken ‘yan sanda.
A cikin bidiyon, an ga wasu jami’an ‘yan sanda suna jinjina wa masu ɗauke da makaman yayin da suke wuce wa.
