
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙasar Afirka ta Kudu ta yi nasarar hayewa zuwa rukunin ‘yan 32 a gasar Kofin Duniya na 2026, a karo na farko a tarihinta bayan doke Koriya ta Kudu da ci 1 da 0 a wasansu na ranar Laraba.
Ƙasar Afirkan ta yi nasarar samun zuwa zagayen ne bayan kammala wasannin rukunin-rukuni na rukuninsu da ke gudana a gasar, inda suka ƙare a matsayi na biyu.
A wani ɓangare kuwa, Brazil ta Nahiyar Amurka ta Kudu ta tsallake zuwa zagayen ne bayan da ta lallasa Scotland da ci 3 da 0, lamarin da ya basu damar samun gurbi a matakin.
Haka ma a Birnin Atlanta, inda Moroko ta su Hakimin ƙungiyar PSG ta doke Haiti da ci 4 da 2, lamarin da ya sa ta haye zuwa zagayen na gaba. Gabanin wasan, Moroko ta buga wasanni 31 ba tare da an doke ta ba a ko ɗaya daga cikinsu.
A yanzu dai Brazil da daɗaɗɗen koci, Carlo Anceloti ke jagoranta na fatan lashe kofin karo na farko acikin shekaru 24 tun bayan da ta ɗauka a 2002.
