Girgizar ƙasa ta yi ajalin mutane da dama da jikkata ɗaruruwa a Venezuela

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu tagwayen girgizar ƙasa sun yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 80 da jikkata 700 da ɗoriya a Venezuela, kamar yadda shugabar riƙo ta ƙasar ta bayyana a ranar Alhamis, lamarin da ya jefa jama’ar yankin cikin firgici.

Akan haka ne jami’an hukumomi da sauran al’ummar ƙasar suka riƙa hawa abubuwa masu tsawo da nufin neman tsira daga iftila’in, lamarin da ya sa jagoran, Delcy Rodriguez ta ayyana dokar ta-ɓaci.

Girgizar ƙasar masu faɗin murabba’i 7.2 da 7.5 sun auku ne a waje guda na Venezuela a ranar Laraba, kamar ya yadda hukumomi suka bayyana, waɗanda suka sanya gine-gine ruftawa da rufe babban filin jiragen saman ƙasar.

A cewar Rodriguez, an sake samun ƙananan girgizar ƙasa guda 20 bayan aukuwar manya biyun, inda hakan ya sa mutane da dama suka shiga ɗimuwa a birnin da koma wa kan titina sun jiran ɗauki.

Shugaba Donald Trump na Amurka a ranar Laraba, ya ce iftila’in da ya samu mutanen kirkin Venezuela babban al’amari ne da ya jefa jama’a cikin ƙunci kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Girgizar ƙasa mafi muni a tarihin ƙasar sune waɗanda aka yi a yankin Arewa maso Gabas a shekarar 1997 da ya yi ajalin mutane 73 da kuma na Caracas a 1967 da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 236.

By Babaji