Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wani gidan yin fina-finai da ke yankin Ɗorayi, Unguwar Bello, a ƙaramar hukumar Gwale bisa zargin karya dokokin tsara birane da kuma yin shi a yankin da aka ware domin gidajen zama na al’umma da iyalai.
Wannan aiki an gudanar da shi ne a ƙarƙashin shirin “Operation Show Your Document”, wanda babban daraktan hukumar tsara taswirar filaye ta jihar Kano (KANGIS), Dalhatu Aliyu Sani, ke jagoranta.
Kazalika, Dr Sani ya ce matakin ya biyo bayan korafe-ƙorafen da mazauna yankin da wasu malamai suka gabatar.
A cewar Dr. Sani binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa gidan bai cika ƙa’idojin doka da ake buƙata ba.
Rufe wannan gida dai ya zo a daidai lokacin da al’umma a yankin ke ci gaba da ƙorafi da rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta cewa samar da gidan na iya zama silar budewar ɓarna ko lalacewar tarbiyya a yankin kasancewar za a tattara mutane kala-kala da ba a san tarbiyarsu ba su zo cikin gidajen al’umma suna rayuwa a wannan yanayi da ake fama da ƙalubale na tsaro a Nijeriya.
