Kwamitin Ilimi na ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) reshen Jihar Katsina ta naɗa Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu, Mallam Bashir Tanimu Gambo, a matsayin Grand Patron na Jihar Katsina.
An gudanar da bikin naɗin ne a ƙarƙashin jagorancin Shugaban JIBWIS na Jihar Katsina, Sheikh Yakubu Musa Hassan (Sautus Sunnah), tare da halartar malamai da sauran manyan baƙi.
A cewar shugabannin ƙungiyar, an yi wa Mallam Bashir Tanimu Gambo wannan naɗi ne bisa la’akari da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa addinin Musulunci da tallafa wa harkokin ilimi, da’awa da sauran ayyukan alheri a faɗin jihar.
Da yake jawabi a wajan taron, Sheikh Yakubu Musa Hassan ya yaba da irin sadaukarwa da jajircewar kwamishinan wajen hidimtawa addinin Musulunci, yana mai cewa irin waɗannan ayyuka ne suka sa ya cancanci wannan matsayi mai girma.
Ya ƙara da cewa Mallam Bashir Tanimu Gambo ya kasance mutum mai kishin addini wanda ke amfani da lokacinsa da dukiyarsa wajen tallafa wa ayyukan da ke inganta ilimin addini da yaɗa koyarwar Musulunci a tsakanin al’umma.
A nasa ɓangaren, Mallam Bashir Tanimu Gambo ya nuna godiyarsa ga shugabannin JIBWIS bisa wannan karramawa da suka yi masa, tare da alƙawarin ci gaba da bayar da gudunmawarsa wajan daukaka addinin Allah.
