An ceto mutum 10 bayan ruftawar gini a Legas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kimanin mutane 10 ne aka ceto bayan samun raunuka a sanadiyyar ruftawar wani gini a yankin Alakija da ke Jihar Legas a safiyar ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar kashe gobara da bayar da agajin gaggawa ta jihar ta ce al’amarin ya faru ne a ranar Alhamis, a yankin hanyar Old Ojo ta madakatar ababen hawa daura da babban titin Legas zuwa Badagry.

Kwantirola Janar ta hukumar, Margaret Adeseye ta ce iftila’in ya rutsa ne da wani gida da ke da mutane da dama suke zama acikinsa, kamar yadda ta shaida a wata sanarwa, ranar Alhamis.

Haka kuma, an gano cewa aƙalla mutane 10 ne aka ceto a raye da suka jikkata, waɗanda tuni aka miƙa su ga jami’an lafiya domin ba su kulawa.

A cewarta, sun tura jami’an kwana-kwana zuwa wajen da abin ya faru yayin da suka samu kiran gaggawa akan al’amarin da misalin ƙarfe 11:49 na safe.

Daga cikin jami’an da suka garzaya zuwa yankin bayan na hukumar akwai na Hukumar kashe Gobara ta Ƙasa, ‘Yan sanda, Sojojin Ruwa, LNSC da kuma NRCS.

By Babaji

Leave a Reply