Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da ƙudirin dokar kafa Rundunar ’Yan Sandan Jihohi bayan karatu na uku a wani gagarumin mataki da ake ganin zai sauya tsarin tsaron ƙasa tare da ba wa jihohi damar taka rawar gani wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
ƙudirin dokar, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa ranar Talata, ya samu amincewa ne a zaman majalisar na ranar Laraba bayan doguwar muhawara da nazari kan gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya da ake buƙata domin tabbatar da aiwatar da sabon tsarin.
Amincewar da majalisar ta bayar na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ke fuskantar matsalolin tsaro da suka haɗa da ta’addanci, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, fashi da makami da sauran manyan laifuka, wanda ya sa ake ci gaba da kira da a karkasa tsarin aikin ’yan sanda domin ƙara kusantar da tsaro ga al’umma.
Yayin da yake gabatar da muhawara kan ƙudirin, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya bayyana ƙudirin a matsayin ɗaya daga cikin muhimman gyare-gyaren tsarin dimokuraɗiyyar Nijeriya tun bayan komawar ƙasar mulkin farar hula.
Ya ce, ƙudirin zai maye gurbin tsarin da ke bai wa Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya kaɗai ikon gudanar da ayyukan tsaro a faɗin ƙasa, inda zai samar da Rundunar ’Yan Sandan Tarayya da kuma Rundunar ’Yan Sandan Jiha ga kowace jiha da ta amince da kafa ta ta hanyar dokar majalisar dokokin jihar.
A cewarsa, ba za a fara aikin Rundunar ’Yan Sandan Jiha a kowace jiha ba har sai an kafa ta bisa doka tare da tabbatar da cewa ta cika ƙa’idoji da sharuɗɗan da Majalisar Tarayya za ta gindaya.
Sanata Bamidele ya bayyana cewa sabon tsarin ba zai rage ƙarfin Rundunar ’Yan Sandan Tarayya ba, domin za ta ci gaba da kula da muhimman batutuwan tsaron ƙasa da suka haɗa da yaƙi da ta’addanci, laifukan yanar gizo, tsaron iyakoki, safarar makamai, laifukan da suka shafi jihohi da dama da kuma kare cibiyoyin gwamnatin tarayya.
Ya ce Rundunar ’Yan Sandan Jihohi kuwa za ta mayar da hankali ne wajen aiwatar da dokokin jiha, tabbatar da zaman lafiya, hana aikata laifuka, binciken manyan laifuka a yankunansu da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Gwamnoni za su naɗa kwamishinoni
ɗaya daga cikin muhimman abin da ƙudirin dokar ta ƙunsa shi ne bai wa gwamnonin jihohi ikon naɗa Kwamishinonin ’Yan Sanda na jihohinsu.
Sai dai ƙudirin ya tanadi cewa naɗin ba zai tabbata ba har sai majalisar dokokin jihar ta amince da shi.
ƙudirin ya kuma tanadi cewa yayin da Sufeto Janar na ’Yan Sanda zai ci gaba da jagorantar Rundunar ’Yan Sandan Tarayya, kowace Rundunar ’Yan Sandan Jiha za ta kasance ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sanda da gwamna ya naɗa kuma majalisar dokokin jihar ta tabbatar.
Har ila yau, dokar ta bai wa gwamnoni damar bayar da umarnin manufofi na tsaro ga kwamishinonin ’yan sandan jihohi ta hanyar rubutu kan batutuwan da suka shafi zaman lafiya da tsaron jama’a a jihohinsu.
Kariya daga cin zarafi:
Duk da fargabar da wasu ke nunawa kan yiwuwar amfani da Rundunar ’Yan Sandan Jihohi wajen murƙushe abokan hamayya na siyasa, ƙudirin ya tanadi matakan kariya domin hana hakan. A cewar ƙudirin, haramun ne a yi amfani da Rundunar ’Yan Sandan Jiha domin manufofin siyasa, ƙabila, addini ko son rai.
Haka kuma, Kwamishinan ’Yan Sandan Jiha ba zai iya kama, tsare ko binciken mutum, jam’iyya ko wata ƙungiya saboda sukar gwamnati kawai ba, sai dai idan doka ta ba da damar yin hakan.
Sanata Bamidele ya ce wannan tanadi ya nuna cewa ƙudirin ya yi la’akari da damuwar da jama’a ke da ita game da yiwuwar amfani da rundunar wajen cin zarafin ’yan adawa ko masu ra’ayi daban-daban.
Majalisar Tarayya za ta sanya ƙa’idoji:
ƙudirin ya kuma bai wa Majalisar Tarayya ikon tsara ƙa’idojin da dukkan rundunonin ’yan sanda za su bi, musamman a fannoni kamar ɗaukar aiki, horo, tantance ma’aikata, ƙarin girma, ladabtarwa, amfani da makamai, karɓar koke-koke daga jama’a da kuma tsarin gudanarwa.
Masu goyon bayan ƙudirin sun bayyana cewa, hakan zai taimaka wajen tabbatar da daidaito da ƙwarewa a ayyukan ’yan sanda a faɗin ƙasar.
Akpabio ya yaba da matakin:
A yayin da yake jawabi bayan amincewa da ƙudirin, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana dokar a matsayin wani muhimmin mataki da zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar.
Ya ce kafa Rundunar ’Yan Sandan Jihohi zai taimaka wajen rage matsalolin garkuwa da mutane, fashi da makami, ta’addanci da sauran laifukan da ke faruwa a matakin ƙananan hukumomi da jihohi.
Sanata Akpabio ya ƙara da cewa sabon tsarin zai kusantar da jami’an tsaro ga jama’a tare da ba da damar samun saurin amsa kiran gaggawa idan wani al’amarin tsaro ya taso.
Masana harkokin tsaro da dama sun bayyana cewa idan aka aiwatar da dokar yadda ya kamata tare da tsauraran matakan sa ido, Rundunar ’Yan Sandan Jihohi na iya zama wani muhimmin ginshiƙi wajen inganta tsaro da ƙarfafa tsarin tarayya a Nijeriya.
ƙudirin yanzu zai ci gaba da sauran matakan da kundin tsarin mulki ya tanada kafin ya zama cikakkiyar doka da za a fara aiwatarwa a faɗin ƙasar nan.
