Gwamna Zulum ya bada umarnin rufe mafi girman sansanin ’yan gudun hijira a Bama

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ba da umarnin rufe sansanin ’yan gudun hijira na cikin gida da ke Bama nan take, wanda shi ne mafi girman sansanin masu neman matsuguni a wajen Maiduguri, babban birnin jihar.

Haka kuma ya bayyana cewa sansanin da ke Gwoza shi ne na gaba da za a rufe cikin makonni masu zuwa.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin wata ziyara da ya kai sansanin ’yan gudun hijira da ke Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Gwoza, inda ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na kawo ƙarshen zaman gudun hijira na dogon lokaci tare da tabbatar da sake tsugunar da al’ummomin da rikici ya raba da muhallansu.

“Jiya mun kai ziyara Bama inda muka sa ido kan tantance ’yan gudun hijira, kuma zuwa ƙarfe 12 na rana ya kamata a rufe sansanin Bama gaba ɗaya,” inji Zulum.

Ya ƙara da cewa, “Yau muna Gwoza, mun riga mun yi wa kowa rajista da tantancewa, kuma da yardar Allah cikin makonni biyu zuwa uku masu zuwa, wannan sansani ma za a rufe shi.”

Gwamnan ya bayyana cewa shirin mayar da jama’a garuruwansu da sake tsugunar da su ya samu nasara ne sakamakon zaman lafiya da ya fara dawowa a yankuna da dama da a baya suke ƙarƙashin ikon mayakan Boko Haram.

A cikin shekaru bakwai da suka gabata, gwamnatin jihar Borno ta samu nasarar sake tsugunar da al’ummomi da dama a ƙaramar Hukumar Bama, ciki har da Darajamal, Nguro Soye, Goniri, Banki, Abbaram, Ngoshe, Kirawa da Warabe, da sauran yankuna a faɗin jihar.

Sai dai Zulum ya nuna damuwa kan yadda ayyukan ta’addanci da sauran laifuka ke ƙaruwa a sansanonin ’yan gudun hijira, yana mai gargaiin cewa wasu daga cikin sansanonin sun fara zama cibiyoyin aikata miyagun laifuka da barazana ga tsaro.

“A yanzu akwai matsalolin aikata laifuka a sansanoninmu. Mun gano masu hannu a ciki, kuma za a mayar da su yankunansu tare da miƙa su ga shugabannin al’ummominsu. Idan ba haka ba, mayaƙan Boko Haram da ISWAP na ci gaba da kutsawa cikin sansanonin,” inji gwamnan.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu mutane ke barin gidajensu suna komawa sansanonin ’yan gudun hijira domin samun tallafin kayan agaji daga ƙungiyoyin agaji masu zaman kansu.

A cewarsa, binciken tantancewar da aka gudanar kwanan nan ya gano adadi mai yawa na mutanen da ba ainihin ’yan gudun hijira ba ne, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta ga ba za ta iya ci gaba da kula da sansanonin a irin wannan yanayi ba.

Gwamnan ya bayyana cewa sansanin Gwoza ne zai zama na gaba da za a rufe a ƙarƙashin babban shirin sake tsugunar da jama’a da gwamnatin jihar ke aiwatarwa.

Ya kuma yi nuni da cewa wasu sansanoni da dama a sassa daban-daban na jihar Borno za a rufe su kafin ƙarewar wa’adin mulkinsa.

“Mutane da yawa da ke zaune a gidajensu suna dawowa sansanonin ne kawai domin karɓar kayan tallafi daga kungiyoyin agaji. Za mu tabbatar cewa komawar jama’a garuruwansu ta kasance mai ɗorewa.

“Shekara guda da ta gabata, wannan sansani ya kusa zama babu kowa, domin ba a samu fiye da gidaje 400 ba. Amma abin mamaki yanzu kusan gidaje 3,000 ne suka dawo sansanin, alhali mafi yawansu mazauna garin ne,” inji shi.

Matakin da gwamnatin jihar Borno ta ɗauka na nuna aniyarta ta ƙara ƙaimi wajen sake tsugunar da mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, tare da ƙarfafa nasarorin da aka samu a yaki da ta’addanci da kuma tabbatar da cewa tallafin jinƙai yana isa ga waɗanda suka cancanta kawai.

By ukarofi

Leave a Reply