‘Yan bindiga sun kashe mutane bakwai a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Al’ummar garin Sayaya a ƙaramar hukumar Matazu na cikin zullumi da fargaba bayan da ‘yan bindiga suka kashe mutane bakwai a cikin garin na Sayaya.

Wani mazaunin garin da baya so a ambaci sunan sa ya ce da safiyar Alhamis misalin ƙarfe 9 na safe sai dai suka ga ‘yan bindiga kan babura sun shigo garin suna ta harbin uwa da wabi.

Ya ce mutane da dama sun gudu zuwa ƙauyukan da suke maƙwabtaka da garin na Sayaya bayan da ‘yan bindigan sun ɗauki tsawon lokaci suna ta harbe harbe a gidaje shaguna da makarantun garin.

Majiyar ya ce mutane bakwai ‘yan bindigan suka kashe da dama suka sami mummunar raunuka na harbe harben bindiga a cikin garin.

Mutanen garin sun shaida cewa sun ɗauki tsawon lokaci suna zaune lafiya bayan da ƙaramar hukumar ta zaman sasanci da ‘yan bindigan kafin wannan lamarin ya faru.

Sun juma zargi ƙasurgumin ɗan bindiga kachalla Muhammadu wanda ke da sansanin sa a yankin Matazu kuma ya daɗe yana cin karansa ba babbaka a yankin.

Kachalla shi ya jagoranci sace da sanadiyar mutuwar marigayi Manjo Janaral Rabe Abubakar Mai ritaya da wasu mutane da dama waɗanda suka garkuwa da su a yankin Matazu.

Daga baya ne rundunar sojojin Najeriya suka yi wa sansanin na Kachalla ƙawanya inda suka kashe ‘yan bindiga da dama wasu suka gudu suna dauke da raunuka daban daban na harbin bindiga har shima jagoran ‘yan bindigan Kachalla ya shige daji ba a sami nasarar kama shi ba.

Mutanen garin sun bayyana cewa wannan ƙazamin harin da ‘yan bindigan suka kai a Sayaya ya biyo bayan janye sojoji daga dazukan Matazu da akayi.

Sun ce lokacin da sojojin sina nan a yankin suna tafiyar da harkokin su na yau da kullum hankali kwance domin a lokacin ‘yan bindigan sun bar yankin,Amma da sojojin suka bar yankin sai ‘yan bindigan suka dawo.

Mutanen garin suka ce ko a kwanan baya Kachalla da mutanen sa sun tare hanyar Karaduwa zuwa Rimaye inda sukai garkuwa da dimbin matafiya da kuma cin zarafin ‘yan ƙauyukan.

Mutanen da ‘yan bindigan suka kashe a garin Sayaya sun haɗa da Abdullahi Mustapha da Yalili mai ruwa, Lawal Chidi, Isau Maharba da Salma Tasi’u sai Ibrahim Uncle wanda ke fama da taɓin hankali.

An riga anyi masu sutura.

By ukarofi

Leave a Reply