Nijeriya ta samu nasarar gano ma’adanai masu daraja a Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta sanar da gano wani katafaren yankin ma’adanai na duniya a Jihar Kaduna, wanda ke ɗauke da ɗimbin ma’adanan platinum, zinari, nickel, tagulla, lithium da kuma wasu muhimman ma’adanai masu daraja da ake kira ‘Rare Earth Elements’.

Ministan Ma’adanai na ƙasa, Dakta Dele Alake, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin buɗe taron zuba jari kan albarkatun ƙasa da makamashi na Afirka karo na biyar (AFNIS 2026), wanda aka gudanar a Cibiyar Taro ta Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja.

Taron, wanda aka gudanar ƙarƙashin taken “Afirka ɗaya, Manufa ɗaya Kan Albarkatun ƙasa”, ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na nahiyar.

Alake ya bayyana wannan nasara a matsayin wani babban ci gaba da zai ƙara ɗaga martabar Nijeriya a kasuwar ma’adanai masu muhimmanci ta duniya.

A cewarsa, Hukumar Binciken ƙasa da Ma’adanai ta Nijeriya (NGSA) ce ta tabbatar da gano waɗannan ma’adanai bayan wani kamfani mai zaman kansa ya gudanar da bincike tare da haɗin gwiwar hukumar.

Ministan ya bayyana cewa wannan ne karon farko da gwamnati ke bayyana wannan labari a bainar jama’a.

“Wannan muhimmin labari ne da ya kamata kafafen yaɗa labarai da masu ruwa da tsaki su lura da shi. Karon farko kenan da nake sanar da hakan a fili. Sabbin binciken da Hukumar Binciken ƙasa da Ma’adanai ta Nijeriya ta tabbatar sun gano wani katafaren yankin ma’adanai na duniya a Kaduna,” inji Alake.

Ya ce yankin na ɗauke da ma’adanai masu inganci ƙwarai da gaske, musamman platinum, zinari, nickel, tagulla, lithium da kuma wasu ma’adanai masu muhimmanci da ake amfani da su wajen samar da makamashi mai tsafta da kuma manyan fasahohin masana’antu.

A cewarsa, wannan ci gaba zai sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake sa ran za su zama manyan wuraren zuba jari a harkar ma’adanai masu muhimmanci a duniya.

Ministan ya ce wannan nasara ta yi daidai da manufar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bunƙasa tattalin arziki ta hanyar ƙarfafa harkar ma’adinai da rage dogaro da albarkatun mai.

Ya bayyana cewa gwamnati na aiwatar da sauye-sauye masu yawa domin jawo masu zuba jari na gari, bunƙasa sarrafa ma’adanai a cikin gida da kuma ƙarfafa bin dokokin da suka shafi harkar.

Alake ya jaddada cewa Nijeriya na ƙoƙarin barin tsohuwar al’adar fitar da ɗanyen ma’adanai zuwa ƙasashen waje ba tare da an sarrafa su ba, tare da mayar da hankali kan ƙara musu ƙima a cikin gida.

“Na dogon lokaci, yalwar ma’adanan Nijeriya ba ta samar wa ƙasar cikakkiyar fa’ida ba. Muna da ɗimbin albarkatu amma ba a sarrafa su yadda ya kamata. Buƙatar duniya tana ƙaruwa amma ba a samu isasshen binciken ƙasa ba. Haka kuma ana fama da matsalolin aiwatar da doka da kuma ayyukan da ba su da tsari,” inji shi.

Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnati ta soke lasisin haƙar ma’adanai guda 924 da ba a amfani da su domin hana masu riƙe da su yin kasuwancin takardu kawai ba tare da haɓaka ayyukan ma’adinai ba.

Ya ƙara da cewa, yanzu gwamnati tana buƙatar duk masu neman lasisin haƙar ma’adinai su gabatar da tsare-tsaren yadda za su sarrafa ma’adanan a cikin gida kafin a ba su izini.

A cewarsa, wannan sabon tsari ya fara haifar da sakamako mai kyau, musamman a ɓangaren sarrafa lithium da sauran muhimman ma’adanai.

Ya bayyana cewa an samu zuba jarin dala miliyan 800 a harkar sarrafa lithium, wanda ya haɗa da gina masana’antar sarrafa lithium ta dala miliyan 600 da kuma matatar lithium ta dala miliyan 200 a kusa da Abuja.

Haka kuma akwai wasu manyan ayyukan da suka haɗa da masana’antar ASBA ta dala miliyan 50 a Babban Birnin Tarayya, aikin sarrafa lithium na Aɓatar na dala miliyan 600 a Jihar Nasarawa da kuma aikin ƙarfe zuwa ƙarafa na dala biliyan ɗaya a Jihar Kogi.

Alake ya ce sauye-sauyen da gwamnati ta aiwatar sun taimaka wajen ƙara kuɗaɗen shiga daga ɓangaren ma’adinai, inda kuɗaɗen shiga suka tashi daga kusan naira biliyan 6 a farkon wannan gwamnati zuwa sama da naira biliyan 38 a shekarar 2024, sannan suka kai kusan naira biliyan 68.1 a shekarar 2025.

Duk da haka, ya bayyana cewa har yanzu waɗannan alƙaluma ba su nuna cikakkiyar damar da ke tattare da harkar ma’adinai a Nijeriya ba, amma ya nuna kwarin gwiwar cewa ci gaba da gyare-gyare, ƙarfafa dokoki da kuma ƙarin zuba jari za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

By ukarofi

Leave a Reply