Kofin Duniya: Moroko ta karya tarihin Super Eagles na ƙasar Afirka mafi yawan ƙwallaye

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙasar Moroko ta kafa sabon tarihi na zama ƙasar Afirka da ta fi yawan ƙwallaye a gasar Kofin Duniya na FIFA, lamarin da ya ba ta damar kere Super Eagles ta Nijeriya.

Ƙasar ta samu nasarar haka ne bayan doke Haiti da ci 4 da 2 a gasar, sakamakon da ya ba ta damar zuwa zagayen ‘yan 32 a gasar.

Waɗannan ƙwallaye da Moroko ta samu sun ba ta damar kere a Nijeriya a matsayin ƙasar da ta fi yawan ƙwallaye a gasar daga ƙasashen Nahiyar Afirka.

A yanzu, Atlas Lions tana da ƙwallo 26 daga wasanni 26 na Kofin Duniya, yayin da Super Eagles take da 23 daga wasanni 21.

Wannan nasara ta biyo bayan bajinta a wasanni da dama da ƙasar ta buga a matakin Nahiya da kuma ƙasa da ƙasa.

By Babaji

Leave a Reply