Atiku ya caccaki Tinubu kan matsalar yunwa da rashin tsaro

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan wasu kalamai da suka nuna cewa kafafen yaɗa labarai ne ke ƙara nuna tsanantar matsalolin yunwa, wahalar rayuwa da rashin tsaro a ƙasar nan.

Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce ’yan Nijeriya ba sa buƙatar ’yan jarida su gaya musu cewa suna cikin yunwa ko wahala domin suna fuskantar waɗannan matsaloli a rayuwarsu ta yau da kullum.

Ya ce, “’Yan Nijeriya ba sa buƙatar ’yan jarida su gaya musu cewa suna cikin yunwa. Uban gida da yake kwana yana tunanin yadda zai samo wa iyalansa abinci ba ya buƙatar rahoton jarida don tabbatar da wahalar rayuwa.”

Atiku ya ƙara da cewa uwa da ke sayen kayan abinci da ninki uku ko huɗu na farashin da take saya shekaru biyu da suka gabata ba ta buƙatar wani shiri na talabijin domin ta fahimci hauhawar farashin kaya.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa ƙoƙarin dora wa kafafen yaɗa labarai alhakin bayyana matsalolin ƙasar alama ce da ke nuna cewa gwamnati ta fara nesanta kanta daga halin da talakawa ke ciki.

A cewarsa, miliyoyin ’yan Nijeriya na fama da tsadar kayan abinci, raguwar ƙarfin saye, rashin aikin yi da kuma matsananciyar wahalar rayuwa.

“Faɗin cewa ana ƙara gishiri kan waɗannan matsaloli raini ne ga miliyoyin ’yan Nijeriya da ke rayuwa cikin ƙunci. Wannan yana nufin ana gaya musu cewa aljihunsu babu kuɗi, bashin da suka kasa biya da kuma gidajensu marasa abinci duk ƙirƙira ce,” in ji shi.

Game da matsalar tsaro kuwa, Atiku ya ce hare-haren da ake samu a sassan ƙasar nan ba ƙirƙirar kafafen yaɗa labarai ba ne.

Ya ce, “Kafafen yaɗa labarai ba su ƙirƙiro kashe-kashen Benue ba, ba su ƙirƙiro hare-haren Filato ba, kuma ba su ƙirƙiro ayyukan ’yan bindiga a Zamfara, Katsina da Neja ba. Haka kuma satar mutane domin neman kuɗin fansa ba ƙirƙirarsu ba ce.”

Atiku ya kuma soki ra’ayin cewa mutane su guji tafiye-tafiye da dare domin kauce wa hare-haren masu garkuwa da mutane, yana tambayar ko hakan na nufin gwamnati ta amince cewa ’yan Nijeriya ba za su iya gudanar da harkokinsu cikin aminci ba sai a wasu lokuta kaɗan na yini.

Ya ce, “Shin gwamnati na nufin tattalin arzikin Nijeriya ya koma na awanni kaɗan ne kawai, inda mutane za su rufe kasuwancinsu kuma su koma gida da zarar rana ta faɗi?”

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada cewa alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma yana kan gwamnati ne, ba kan jama’a ba.

A cewarsa, abin da ’yan Nijeriya ke buƙata shi ne ɗaukar matakan magance matsalolin tsaro da tattalin arziki, ba yawan bayar da shawarwari ko ɗora alhaki kan kafafen yaɗa labarai ba.

Atiku ya kuma kare aikin ’yan jarida, yana mai cewa aikinsu shi ne bayyana gaskiya da kuma isar da muradun al’umma ga masu mulki.

“Zargin kafafen yaɗa labarai saboda sun ba da rahoton matsalolin ƙasa kamar zargin ma’aunin zafi ne saboda ya nuna mutum na da zazzaɓi,” inji shi.

A ƙarshe, ya buƙaci gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali wajen samar da mafita ga matsalolin da ke addabar ’yan Nijeriya.

“Nijeriya ba ta buƙatar bayanin dalilin wahala. Nijeriya na buƙatar mafita. Ba ta buƙatar darasi kan yadda mutane ke kallon abubuwa. Nijeriya na buƙatar sakamako,” inji Atiku.

By ukarofi

Leave a Reply