Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta yi watsi da zargin da ke cewa ta dauki nauyin wasu shugabannin ’yan bindiga zuwa aikin Hajjin bana, tana mai bayyana zargin a matsayin ƙarya, sharri da kuma yunƙurin yaudarar al’ummar jihar.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Cikin Gida da Tsaro na Jihar Katsina, Dr. Nasiru Mu’azu Danmusa, ya sanya wa hannu, gwamnatin ta mayar da martani kan ikirarin da wani mutum mai suna Bashir Kurfi ya yi a wata kafar yaɗa labarai cewa gwamnatin jihar ta dauki nauyin wasu shugabannin ’yan bindiga zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji.
Sanarwar ta bayyana cewa zargin ba shi da tushe balle makama, tana mai cewa an yi shi ne domin bata sunan gwamnati da kuma kawo cikas ga ƙoƙarin da take yi tare da hukumomin tsaro wajen samar da zaman lafiya a jihar.
Dr. Danmusa ya ce zargin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnati da jami’an tsaro ke samun gagarumar nasara a yaƙi da ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a sassa daban-daban na jihar Katsina.
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda wasu mutane ke amfani da batutuwan tsaro wajen cimma muradunsu na siyasa ko na kashin kai, ba tare da la’akari da illar hakan ga zaman lafiya da haɗin kan al’umma ba.
Kwamishinan ya ƙalubalanci mai wannan zargi da ya fito da hujjoji da shaidu da za su tabbatar da ikirarinsa. Ya gargaɗi cewa idan har ba a gabatar da hujjoji ba, gwamnati za ta ɗauki matakin shari’a domin kare mutuncinta da kuma tabbatar da cewa masu yaɗa ƙarya sun fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
“Gwamnatin Jihar Katsina ba za ta zura ido tana kallon yadda ake yaɗa ƙarya da sharri da nufin bata mata suna ba. Duk wanda ya yi irin wannan zargi dole ne ya gabatar da hujjoji ko kuma ya fuskanci sakamakon abin da ya aikata,” in ji sanarwar.
A ƙarshe, gwamnatin ta yi kira ga al’ummar jihar da su yi watsi da irin waɗannan rahotanni marasa tushe, tare da ci gaba da bai wa gwamnati, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki cikakken goyon baya a ƙoƙarin da suke yi na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar Katsina.
