Tsaro: Da zaɓina ne zan hana saka baƙin gilashin mota – Sufeto Janar

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sufeto Janar na Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu, ya bayyana cewa da ikon hakan yana hannunsa, da ya haramta amfani da dukkan motocin da ke da baƙin gilashi, wato tinted ɓehicles, a faɗin ƙasar nan saboda barazanar tsaro da yake ganin suna haifarwa.

Disu ya yi wannan bayani ne a ranar Talata a Abuja yayin da yake mayar da martani ga damuwar da Shugaban ƙungiyar Lauyoyi ta ƙasa, Afam Osigwe, ya nuna game da tsarin sabunta lasisin baƙin gilashi da kuma yadda ake tara kuɗaɗen da suka shafi wannan izini.

“Ni ina da wata fahimta daban kan wannan batu. A halin yanzu muna fuskantar ƙalubalen tsaro a ƙasar nan. Da a ce ni kaɗai ne zan yanke hukunci, babu wata mota mai baƙin gilashi da za a bari a Nijeriya. Kuma muna kan hanyar cimma hakan,” inji Sufeto Janar.

Ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane, ’yan fashi da makami da kuma masu aikata fashin ‘one-chance’ na yawan amfani da motocin da ke da baƙin gilashi wajen aikata laifuka, lamarin da ya sa ya ɗauke su a matsayin babban barazana ga tsaro.

Disu ya tuna cewa lokacin da yake riƙe da muƙamin Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya Abuja, binciken da aka gudanar ya nuna cewa yawancin motocin da ƙungiyoyin one-chance ke amfani da su suna da baƙin gilashi.

A cewarsa, daga cikin motoci 27 da jami’an tsaro suka ƙwato daga hannun masu aikata irin waɗannan laifuka, galibinsu suna da gilashin da ba sa ba da damar ganin abin da ke cikin motar.

Sufeto Janar ɗin ya kuma nuna damuwa kan yadda ake amfani da baƙin gilashi masu matuƙar duhu a gaban mota da kuma a bayan mota, yana mai cewa hakan na kawo cikas ga ayyukan jami’an tsaro.

Ya bayyana cewa irin waɗannan gilashai na hana jami’an tsaro gano waɗanda ke cikin mota yayin binciken hanya, lamarin da ke ƙara jefa jami’an cikin haɗari.

Disu ya jaddada cewa doka ta amince ne kawai da amfani da baƙin gilashi ga mutanen da ke da dalilan tsaro ko matsalolin lafiya na musamman, amma ko a irin wannan yanayi bai kamata gilashin ya rufe gani gaba ɗaya ba.

Ya ƙara da cewa, Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya za ta ƙara ƙaimi wajen kama masu amfani da motocin da ke da baƙin gilashi ba bisa ƙa’ida ba a sassan ƙƙasar.

Tun da farko, Shugaban ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya, Afam Osigwe, ya bayyana cewa ƙungiyar ba ta adawa da tsarin kula da lasisin gilashin baki, amma tana adawa da mayar da tsarin hanyar tara kuɗaɗen shiga.

Ya yi tambaya kan dalilin da ya sa ake buƙatar sabunta lasisin lokaci zuwa lokaci, yana mai cewa idan an adana bayanan abin hawa a cikin tsarin bayanai, babu buƙatar maimaita sabuntawa.

Har ila yau, ya soki yadda aka bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar karɓar kuɗaɗen lasisin a madadin Rundunar ’Yan Sanda.

Sai dai Osigwe ya bayyana cewa ƙungiyar tana goyon bayan ɗaukar mataki kan motocin da gilashinsu ke hana jami’an tsaro ganin waɗanda ke cikinsu gaba ɗaya.

A watan Disamban bara ne ƙungiyar lauyoyi ta soki ’yan sanda bayan rundunar ta sanar da dawo da aiwatar da dokar lasisin baƙin gilashi da aka dakatar a baya.

Rundunar ta bayyana cewa za ta fara aiwatar da dokar daga ranar 2 ga Janairu, 2026, tana mai danganta matakin da ƙaruwar laifukan da ake aikatawa ta amfani da motoci a sassan ƙasar.

By ukarofi

Leave a Reply