Peter Obi ya shiga tsaka-mai-wuya bayan kotu ta soke rajistar NDC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A wani mataki da ake ganin babban koma-baya ne ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, wata Babbar Kotun Tarayya a Lokoja ta soke hukuncinta na baya da ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi wa NDC rajista a matsayin cikakkiyar jam’iyyar siyasa.

Mai shari’a Isah Dashe ne ya yanke hukuncin bayan ya amince da ƙorafin da jam’iyyar Peace Movement Party (PMP) ta shigar, ranar Juma’a.

Da wannan hukunci, umarnin da kotun ta bayar a baya na tilasta wa INEC rajistar jam’iyyar NDC ya zama babu tasiri, lamarin da ka iya haifar da ƙalubale ga shirin jam’iyyar na shiga harkokin siyasa a hukumance.

A baya ne wata babbar Kotun Tarayya ta yanke irin hukuncin akan wasu jam’iyyu ciki har babbar jam’iyyar adawa ADC. Sauran sune APP, AA, AP, da ZLP.

A cewar kotun, jam’iyyu sun gaza cika sharuɗɗa da ƙa’idojin shiga zaɓen 2027 bayan rashin kataɓus a babban zaɓen 2023.

By Babaji

Leave a Reply