Har yanzu INEC ba ta samu kuɗin zaɓe ba yayin da wa’adin Yuli ya ƙarato, ta ce za ta yi zaɓen shugaban ƙasa na gwaji

Spread the love

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa INEC, ta bayyana cewa har yanzu ba ta karɓi kuɗaɗen da aka ware domin gudanar da babban zaɓen shekarar 2027 ba.

Kwamishinan INEC mai kula da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a da yaɗa labarai, Mohammed Haruna ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja.

Ya ce duk da cewa ba a saki kuɗaɗen ba, hukumar ta fara shirye-shiryen zaɓen 2027, ciki har da sayen sabbin na’urorin tantance masu kaɗa ƙuri’a na BVAS da maye gurbin waɗanda suka lalace ko suka ɓace a zaɓukan baya.

Haruna ya bayyana cewa dokar zaɓe ta 2026 ta tanadi a saki kuɗaɗen zaɓe akalla watanni shida kafin babban zaɓe, yana mai cewa har yanzu lokaci bai kure ba.

Ya ƙara da cewa jami’an hukumar sun fara tattaunawa kan sayen kayan aiki daga ƙasashen waje, yayin da kuma ake shirin gudanar da gwajin amfani da fasahar zaɓe domin kauce wa matsalolin fasaha irin waɗanda suka shafi tsarin IReV a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Game da tsadar gudanar da zaɓe, Haruna ya ce kasafin kuɗin da INEC ta gabatar na sama da naira biliyan 800 ba shi da yawa idan aka kwatanta da yawan masu kaɗa ƙuri’a da kuma yadda yawancin kayan aikin zaɓe ake shigo da su daga ƙasashen waje.

Ya kuma nuna damuwa kan umarnin kotuna da ke zuwa a ƙarshe kafin zaɓe, yana mai cewa hakan na kawo cikas ga shirye-shiryen hukumar da tsarin fasahar zaɓe.

Dangane da zargin satar bayanan INEC, jami’in ya tabbatar da cewa an dakatar da wani jami’in zaɓe da ake zargi da fitar da wasu bayanai ba bisa ƙa’ida ba, yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da bincike.

Har ila yau, ya yabawa yadda aka gudanar da zaɓen gwamnan Ekiti, inda ya ce na’urorin BVAS sun yi aiki yadda ya kamata, sai dai ya nuna damuwa kan ci gaba da sayen ƙuri’u.

A nasa ɓangaren, daraktan cibiyar PAACA, Ezenwa Nwagwu, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin kuɗaɗen zaɓe, yana mai gargadin cewa jinkiri kan haifar da matsaloli da kuma rage amincewar jama’a da tsarin zaɓe.

By Babaji

Leave a Reply