Ban ga tsananin yunwar da ‘yan Nijeriya ke magana a kai ba – Onanuga

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce ba ya ganin irin matsanancin yunwar da wasu ‘yan Nijeriya ke korafi a kai, yana mai cewa manufofi da gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnatin tarayya na fara haifar da amfani ga jama’a.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa, da yake magana a tashar Arise TV, Onanuga ya ce an ƙirƙiri tunanin cewa yunwa ta mamaye ƙasar tun bayan hawan gwamnatin Tinubu, yana mai cewa mutane da dama na cin gajiyar shirye-shiryen gwamnati.

Ya bayyana cewa yana tambayar ma’aikatansa halin da suke ciki, kuma bai ga irin matsalar yunwar da ake ta magana a kai ba.

Onanuga ya kuma yabawa ayyukan more rayuwa da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa, inda ya ce sabbin hanyoyi da ake ginawa sun rage lokacin tafiye-tafiye, musamman hanyar Lagos zuwa Calabar da kuma hanyar Ijebu-Ode.

Ya ce shirye-shiryen bayar da rancen karatu na NELFUND da kuma rancen kuɗi ta CreditCorp suna taimakawa ɗalibai da ma’aikata, domin suna ba su damar samun rance cikin sauƙi.

Game da matsalar tsaro, Onanuga ya zargi kafafen yaɗa labarai da ƙara yawan rahotannin rashin tsaro ta yadda ake nuna kamar duk ƙasar na cikin haɗari, yana mai cewa akwai matsalolin tsaro a wasu wurare amma ba a ko’ina ba.

Har ila yau, ya soki kalaman ɗan siyasa Peter Obi kan harkar wutar lantarki, yana mai cewa ƙarfin samar da wuta a ƙasar ya ƙaru, sai dai matsalar samar da iskar gas da bashin da kamfanonin wutar lantarki ke bin kamfanonin gas ne ke ci gaba da kawo cikas a fannin.

By ukarofi

Leave a Reply